Mazaunan karamar hukumar Mangu a jihar Filato sun bayyana cewa duk da dokar hana walwala na awa 24 da gwamnati ta saka ranar Talata ‘yan bindiga sun ci gaba da kai wa mutane hari a karamar hukumar ranar Laraba.
Gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya saka dokar hana walwala a karamar hukumar ne domin kawo karshen rikicin da ya barke a yankin ranar Talata.
Uba Shehu wani mazaunin kauyen Mangu Alle ya ce ricikin wanda ya barke tsakanin Fulani makiyaya da manoma ya yi sanadiyyar rikici da hare haren ƴan bindiga a yankin.
Sai dai Shehu ya ce maharan ba su shiga kauyen su a ranar Talata.
Shugaban kungiyar matasa ƴan kabilan Mwaghavul MYM Sunday Dankaka ya ce ba zai iya magana ba saboda ana kai musu hari.
Kakakin gwamnan jihar Gyang Bere ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa gwamnati na kokarin kawo karshen rikicin.
“Har yanzu dokar hana walwalan na aiki kuma gwamnati za ta hada hannu da sarakunan gargajiya domin kawo karshen rikicin.
Mazauna karamar hukumar sun ce
Maharan sun kona coci-coci da masallatai dake Anguwan Dawo, Old Market da Bayan Kasuwa a karamar hukumar sannan har yanzu babu wanda ke da masaniya kan yawan mutanen da aka kashe.
“Babu wanda ke da masaniyar yawan mutanen da aka kashe jiya. Wasu na kwance a asibitoci sannan wasu an kashe su a kauyen Gangara Kwata.
Shehu ya ce maharan sun zo daga Mangu ta Arewa suna shiga Gangara Kwata inda suke cewa mazaunan kauyen da su fito da duk Fulanin da suka ɓoye a kauyen.
Ya ce daga nan sai rikicin ya yadu zuwa wasu bangarorin kauyen inda har aka kona masallatai da shaguna.
Majiya da dama a karamar hukumar sun tabbatar cewa rikicin ya samo asali ne dalilin wasu abubuwan biyu da suka faru ranar Litini.
Wani dan kasuwa da baya so a fadi sunnan sa ya ce rikicin ya auku bayan wani dan sabanin da ya faru tsakanin wani dan kabilar Mwaghavul da wani Bafulatani makiyayi.
“ Wannan bamwangjavul ya buge daya daga cikin shanun Bafulatanin da babura da a dalilin haka Bafulatanin ya kwade mutumin da sanda.
Sojojin sun shiga tsakanin su inda har suka sassanta su.
Discussion about this post