Cacan baki ya kaure tsakanin kasashen Amurka da Birtaniya kan wanene gwanin haɗa ganyen shayi a duniya.
Hakan ya biyo bayan ikirari da wata Farfesa a fannin ilimin sanadirai mai suna, Michelle Francl, wacce ta ce ya kamata a riƙa kara gishiri kadan domin a ganyen shayi don gamsarwa.
Sai dai kuma jin kaɗan bayan fueta haka sai ofishin jakadancin Amurka dake Birtaniya ta nesanta kanta da wannan farfesa da abinda ta ke ikirari a kai.
” Ganyen shayi na daga abubuwan da suka kara karfin dangantakar mu. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba saboda irin wannan kalamai da ba shi da ma’ana da kan gado. in ji ofishin jakadancin.
” Ba ma tare da wannan farfesa da shirmenta na kara gishiri a ganyen shayi idan za a hada shi. Amurka ba ta tare da ita a wannan tarkace na ta. Yayin da ta ce shi dai shayi ya fi daɗi idan aka dafa shi a na’urar ɗunɗuma abinci, wato Microwave.
“Idan dai a harkar haɗa shayi ne, muna nan tare, babu abin da zai shiga tsakanin nu. Za mu ci gaba da dafa shayin da na’urar Microwave.
A martani da Birtaniya ta bada, ta ce abinda Amurka ta yi ya yi daidai, sai dai shayi a safa shi a buta shine shayi ba a tukunya ko a Mirowave ba.
Discussion about this post