Ganin yadda gagarimar matsalar tsaro ta sake kunno kai gadan-gadan, har ta mamaye Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja, sai Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya kira Shugabannin Ɓangarorin Tsaro domin wani taron gaggawa a ranar Talata.
To irin wannan taro dai shugabannni sun sha yin sa a duk lokacin da wata matsala irin haka ya faru, amma ba a tsinana komai, sai dai shan shayi, idan ma har an sha ɗin.
A ƙarshen Taron Majalisar Hukumar ‘Yan Sanda wanda Tinubu ya jagoranta cikin watan Oktoba, 2023, ya kafa Kwamitin Yi Wa Dokoki Garambawul, domin a sake fasalin tsarin aikin ‘yan sanda.
Daga cikin abin da za a duba yayin kwaskwarimar, su ne batutuwan da ake samun sakaci a ɓangaren gyara, yin aiki tare tsakanin hukumomin tsaro, amfani da kayan aiki na zamani da sauran su.
Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun wanda ya halarci taron, ya ce rabon da a sauya wa aikin ‘yan sanda tsari da fasali tun 1891.
Mambonin kwamitin sun ƙunshi Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Musamman a Fannin Tsaro, Nuhu Ribadu, Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Ibrahim Geidam, tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Solomon Arase, wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar Aikin ‘Yan Sanda, sai kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Abdulrahman AbdulRazaq na Kwara.
To Shugaba Tinubu dai tilas ya razana da wannan lamari. A babban birnin tarayya Abuja, kusa da shi, an kwashe yara ‘yan mata shida ‘yan gida ɗaya tare da mahaifin su.
Wani lauya mai suna Oladosu Folorunsho Ariyo, ya yi kururuwar ‘yan bindiga sanye da kayan sojoji sun ɗauke abokin aikin su a rukunin gidajen su, a Abuja, kuma sun haɗa da ‘ya’yan sa huɗu da matar sa, a ranar 7 ga Janairu. Abin takaici har sun kashe ɗan sa na uku, mai suna Michelle, saboda sun nemi Naira miliyan 60, amma an kasa haɗa masu.
Duk da haka mahaifin na su ya haɗa Naira miliyan 7 da kyar, amma ko saurarar sa ba su yi ba.
Kai ko ina fa hala ake fama a faɗin ƙasar nan, ba a Abuja kaɗai ba.
Saboda ko kisan mutum 198 da aka yi lokacin Kirsimeti a Filato, ya isa ya gigita Shugaban Ƙasa har ya tashi ya ɗauki tsatstsauran mataki.
Irin tsarin ‘yan sanda da muke da shi yanzu a Najeriya ba zai magance mana komai ba.
Kafin nan, Shugaban Ƙasa ya nuna yiwuwar ya ƙara yawan ‘yan sanda, waɗanda a yanzu 300,000 kaɗai da ɗoriya. To ƙalubalen da ake fuskanta ya wuce haka.
Idan ba a gaggauta gyara kundin tsarin mulki ba, to Tinubu zai ci gaba da kwasar buhun kunya daga ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi.
Shi kan sa tsarin aikin ‘yan sandan cike ya ke da harɗa-harɗa da harƙalla. Saboda ana samun ɓatagari da ‘yan fashi na shiga ko ana shigar da su aikin ɗan sanda.
Kuma ƙididdigar Hukumar NBS, wato Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, ta ce rundunar ‘yan sanda ce mafi lalacewa wajen harƙalla.
Cikin wasu shekaru goma baya zuwa 2018 jihohi 36 sun kashe Naira tiriliyan 2 wajen ‘yan sanda, kamar yadda Kungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF ta bayyana.
Saboda haka a yanzu ya-kamata NGF ta goyi bayan kafa ‘yan sandan jihohi, domin a magance matsalar tsaro.
Najeriya fa na buƙatar ‘yan sandan zamani, masu kayan aikin zamani a kowace jiha.
Ya kamata Tinubu ya miƙe tsaye, ya nuna da gaske ya ke yi. Kada ya zauna zaman-dirshan ya ce daga zaune zai yaƙi matsalar tsaro, kamar yadda Buhari ya riƙa yi.
Discussion about this post