Aƙalla mutum bakwai suka rasa rayukan su yayin da suka taka nakiyar da Boko Haram suka dasa a kan hanyar Maiduguri zuwa Gamboru Ngala, a Jihar Barno.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Barno, Nahun Daso, ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Waɗanda lamarin ya ritsa da su na cikin wata wata mota ne a lokacin da motar da suke ciki ta taka nakiyar.
Wani mazaunin garin Gamboru Ngala mai suna Yusuf Mari, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa kwanan nan ana ta fama da samun yawaitar motocin da nakiyar Boko Haram ke lalatawa a kan hanyar.
Sufurtandan ‘Yan Sanda Daso, ya shaida cewa nakiyar da ta kashe matafiyan bakwai a hanyar Gamboru Ngala, lamarin ya faru ne a ranar 9 ga Janairu wajen ƙarfe 9:30 na safiya.
“Buɗaɗɗiyar mota ce ƙirar Isuzu ta taso daga Gamboru Ngala da niyyar zuwa Maiduguri, sai ta taka nakiyar kan hanya tsakanin Kinoba da Mosuseni.
“Direban motar da mutum shida da ke tare da shi duk sun mutu nan take, wasu mutum uku samu raunuka.
“Jami’an ‘Yan Sandan Kwance Nakiyasun isa wurin domin nazarin yadda lamarin ya afku,” cewar Daso kuma ya ce ana ci gaba da bincike.
Duk da irin ƙoƙarin da jami’an tsaro ke kan yi, har yanzu Boko Haram sai ƙara yunkurowa suke yi, su na kai kai hare-hare a kan matafiya da mazauna yankunan karkara a Barno.
Ko a ranar Murnar Sabuwar Shekara sai da Boko Haram suka kashe mutum 12 a garin Chibok, Jihar Barno.
Discussion about this post