A karon farko bayan shekaru 12 ya na jan ragamar mafi ƙasaitacciyar attajiran Afrika, Aliko Ɗangote a yanzu ya koma na biyu, yayin da shahararren attajirin Afrika ta Kudu, Johann Repert da iyalan sa suka haye matsayin na ɗaya mafi ƙarfin arziki a Afrika.
Sabon lissafi da ƙididdigar da mujallar Forbes ta gudanar kwanan nan, ta tabbatar cewa Rupert ne na 1 a Afrika, kuma shi ne na 201 a duniya. Shi kuwa Ɗangote ya koma na biyu a Afrika, a duniya kuma shi ne na 219.
Aliko Ɗangote ya shafe shekaru 12 a jere a matsayin biloniyan da ya fi kowa ƙarfin arziki a Afrika.
Sai dai kuma a ƙarshen 2023 darajar Naira wadda ta ragu da kusan kashi 40 bisa 100 tun daga watan Yuni 2023, ta sa darajar ƙarfin arzikin Ɗangote ya ragu idan aka auna Dala da kuma Naira.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Naira ce sahun gaba na kuɗaɗen ƙasashen duniya mafi faɗuwar daraja a 2023.
Rahoton ya ce kuɗin ƙasar Labanon da na Argentina ne na ɗaya da na biyu wajen rashin daraja a duniya. Na ukun su ita ce Naira, a cikin kuɗaɗen ƙasashe 151 da Blooberg ta yi nazari kwanan nan.
Yanzu haka dai an ƙiyasta cewa darajar ƙarfin Ɗangote ya kai dala biliyan 9.5
Johann na Afrika ta Kudu wanda shi ne na ɗaya yanzu a Afrika, ƙasaitaccen mai sayar da kayan alatu da kayan ƙwalisa ne a duniya.
Discussion about this post