Gwamnan jihar Kaduna ya sha alwashin ci gaba da baiwa addinin musulunci gudunmawa da taimako da take bukata domin daukakatar a jihar da kasa baki daya.
Gwamna Sani ya bayyana ahaka a wajen taron wa’azin Kasa wanda ya halarta a Birnin Zaria, ranar Asabar.
A jawabin sa gwamnan ya ce a tsawon shekarun sa na dan siyasa burin sa shine ya tabbatar da ganin duk wani abu da zai yi ya jibanci ci gaba addinin musulci a jihar Kaduna da Kasa baki daya.
” Ina tabbatar muku da cewa ba zan yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da ganin musulunci da karatun alkur’ani a wanzu a cikin al’umman mu baki daya.
Daga nan sai gwamna Uba ya yi wa wadanda suka yi nasara a gasar karatun Alkur’ani na kasa da aka yi a jihar Yobe albishir din cewa zai kaisu aikin Haji na bana.
” Ina so a sanarwa yan kaduna shida da suka yi zarra a gasar karatun Alkur’ani da aka yi a jihar Yobe, cewa ni gwamna Uba, naga Aljihuna ba na gwamnati ba, zai kai su aikin hajji na bana, kyauta.
Sannankuma wuraren koyon sana’a da aka gina a Kaduna, zan karisa shi, in saka kayan aiki, da na koyon sana’a kyauta daga aljihu na ba na gwamnati ba.
Discussion about this post