Kungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), ta bayyana cewa Sojojin Mulkin Nijar kunnen-ƙashi gare su, domin har yanzu sun ƙi sakin hamɓararren Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum da iyalan sa.
Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, a wurin taron da ake kan yi na ƙungiyar ECOWAS.
Touray ya ce Sojojin Mulkin Nijar waɗanda suka ƙwace mulki cikin watan Yuli, su ne shisshigi a ayyukan jinƙai da ake yi a Nijar, wanda ECOWAS ta amince a riƙa yi cikin ƙasar, tun bayan ƙaƙaɓa wa ƙasar takunkumi da ECOWAS ta yi.
A jawabin sa na buɗe taro, Touray ya ce ECOWAS ta ɗan bayar da iznin ɗage kaɗan daga takunkumi, domin bayar da iznin shiga Nijar da magunguna da kayayyakin agaji ga jama’a.
Kowace shekara ƙungiyoyin bada agaji da jinƙai, ciki har da ta Medicins Sans Frontieres (MSF), su na bada magunguna ga aƙalla yara ƙanana 400,000.
Akwai aƙalla mutum miliyan 3.3 na fama da rashin abinci a Nijar.
A wani labarin kuma, Kotun ECOWAS ta yi biris da roƙon da Nijar ta yi a janye mata takunkumi.
Kotun Sauraren Ƙorafe-ƙorafe ta Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) da ke Abuja, ta kori ƙara da roƙon da Jamhuriyar Nijar ta shigar, inda ta nemi kotun ta tilasta ECOWAS ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Jamhuriyar Nijar.
An ƙaƙaba wa Nijar takunkumi ne bayan sojoji sun kifar da gwamnatin farar hula ta tsohon shugaban ƙasa Mohammed Bazoum a cikin watan Agusta.
Duk da kotun ta ce ta na da iznin sauraren ƙarar, to amma kuma ta ce ba za ta iya bada umarnin a janye wa Nijar takunkumi ba.
Shugaban kotun, Edward Asante, wanda ya jagoranci alƙalai uku wajen sauraren ƙarar da yanke hukunci, ya ce Sojojin Mulkin Nijar sun kasa shigar da ƙarin bayanan da kotun ta nema a buƙatun da suka bijiro a kotun.
An yi wannan hukunci a ranar Alhamis, a zaman da alƙalan uku suka yi a Kotun ECOWAS da ke Asokoro, Abuja.
Sauran alƙalan sun haɗa Gberi-be Ouattara da kuma Dupe Atoki, duk sun amince ta ƙin cire wa Nijar takunkumi.
A ranar 26 ga Yuli ce Sojojin Nijar a ƙarƙashin Abdourahmane Tchiani suka kifar da gwamnatin Bazoum.
Daga nan take Shugaban ECOWAS, Bola Tinubu na Najeriya ya jagoranci ƙaƙaba wa Nijar takunkumi.
Najeriya ta rufe iyakokin ta da Nijar, kuma ta katse wa Nijar wutar lantarki a baki ɗayan ƙasar.
Dama daga Nijeriya ake bai wa Nijar wuta.
Takunkumin dai ya janyo ƙarin raɗaɗin tsadar rayuwa a Nijar da kuma Arewacin Najeriya, musamman a jihohi bakwai da suka yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Cikin makon da ya gabata ne Sanatocin Arewa suka yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya maida wa Nijar wutar lantarkin da aka katse mata, domin takunkumin ya na shafar harkokin kasuwanci da tattalin arzikin Arewa.
Discussion about this post