Gogarman ɗan sababin ta’addanci, garkuwa da safarar muggan makamai, kuma wanda aka fi tsoro, Halilu Sububu, ya faɗaɗa aika-aika da ɓarnar da ya ke yi a yankin Arewa maso Yamma.
Sububu wanda ya fara kafa fitinar sa ta hanyar safarar muggan bindigogin da suka haɗa da AK-47, A-yi-ta-ta-ƙare da tashi-gari-barde waɗanda ake girkawa a ƙasa a rataya masu jigidar harsasai, a yanzu ya kafa katafaren sansanin haƙar ma’adinai a dajin Bagega mai albarkatun ƙasa da kewayen dajin Sumke cikin Ƙaramar Hukumar Anka, a Jihar Zamfara.
Asalin Halilu Sububu, haifaffen garin Sububu ne, cikin Ƙaramar Hukumar Maradun. Daga baya ya koma yankin Anka, ya na kamfatar albarkatun ma’adinai a sansanonin haƙar ma’adinai da ya kafa a dajin Sumke.
Yadda shi kaɗai ya fito ya gabagaɗi ya ke wannan harkar haƙar ma’adinai, kuma ya kankane, hakan na fassara irin yadda sauran manyan ‘yan bindigar yankin arankatakaf ke tsoron sa.
Binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar da Dubu ya kafa sansani a yammacin Bagega, inda shi ne ‘gwamnatin’ ƙauyukan da ke yankin, kuma ya na haƙar ma’adinai a dukkan wuraren ma’adinan wurin.
Duk da cewa akwai wasu riƙaƙƙun ‘yan bindiga da ke aikin haƙar ma’adinai a yankin, amma dai babu wanda ke da katafaren fili kuma inda albarkatun ma’adinai suke na maƙudan kuɗaɗe, kamar wuraren da Sububu ya kankane.
Wani matashi da ya daɗe ya na yi wa Halilu Sububu aikin haƙar ma’adinai, ya shaida wa PREMIUM TIMES a cikin Nuwamba cewa, akai-akai Sububu na tura yaran sa su kamo mutanen karkara a kai su su yi masa aikin haƙar ma’adinai.
“Koda yaushe ya na tilasta mu yi masa aikin bauta a ganar sa. Wasu lokuta za a je a kamo mu, mu yi aikin bauta. Wasu lokuta kuma a kan ɗan ba mu ɗan kuɗin da bai taka kara ya karya ba. Yawanci ba kuɗi ki zinari suke biyan mu ba.”
Kafin Sububu ya gane daɗin harkar ma’adinai, babu ruwan ‘yan bindiga da harkar ma’adinai, sai dai mutanen karkara masu haƙar ma’adinai su ɗauke su aikin kula da wurin, su biya su da kuɗi ko da zinari.
Amma yanzu wannan tsohon zance ne. Manyan ‘yan bindiga irin su Sububu sun raina ladar da ake biyan su idan sun tsare wuraren Ma’adinai. Yanzu sun ƙwace harkar haƙar ma’adinai daga hannun mutanen yankunan karkara, sai su riƙa kamo su domin su riƙa yi masu aikin bautar haƙo masu ma’adinai.
,’Yan bindiga sun yanke shawarar shiga kane-kane a harkar haƙar ma’adinai domin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗi, saboda a yanzu dukkan yankunan da suke kaiwa hare-haren, sun daina samun kuɗin fansa, saboda sun tsiyata mazauna yankunan.” Haka manazarci Murtala Ahmad-Rufai mai nazarin ta’addancin ‘yan bindiga ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Halilu Sububu: Gogarman Da Ya Gaji Fashi Da Ta’addanci Daga Wurin Mahaifin Sa:
Shin wane ne Halilu Sububu. To Halilu dai ba ɓarawon sane irin masu yankan aljihu a kasuwa ba ne. Shi kaɗai ne ɗan ta’addar da ke Yankin Arewa maso Yamma, wanda ya yi alaƙa da ‘yan Boko Haram na yankin Sahel, ƙasashen Yammacin Afirka, masu magana da harshen Faresanci, irin su Mali, Nijar, Burkina Faso da Senegal.
An tabbatar cewa ya samu nasibin maƙudan kuɗaɗe a lokacin da ya ke safarar muggan makamai, saboda alaƙar sa da ‘yan ta’addar Sahel.
Ya taɓa yin hira sau ɗaya da ‘yan jarida, inda ya bayyana kan sa cewa shi ne “shugaban ‘yan bindigar Arewa.”
Wani abokin Halilu tun daga yarintar su, wanda PREMIUM TIMES ta yi hira da shi a cikin Oktoba, ta wayar tarho, ya ce An haifi Halilu cikin 1986, aka raɗa masa suna Halilu Jammare. Mahaifin sa Bafulatani ne makiyayi, shi kuma a rugar Jajjaye kusa da Sububu aka haife shi.
Mahaifiyar Halilu ‘yar asalin Jamhuriyar Nijar ce, wadda kakan ta ya zo da ita Najeriya daga Maraɗi, cikin Jamhuriyar Nijar.
“Ta na kamar shekaru 11 ko 12 aka zo Najeriya da ita. Sai masu iko a Sububu suka ba shi wuri ya yi gida. To a lokacin ne Jammare ya gan ta, har aka aura masa ita. Kamar yadda nahiyar PREMIUM TIMES ya tabbatar.
Mahaifin Halilu Riƙaƙƙen Ɗan Fashi Ne:
Mahaifin Halilu ya rasu kamar shekaru 25 da suka gabata. Ya watsar da kiwo ya shiga fashi, kuma abokin riƙaƙƙen ɓarawon yankin ne a lokacin, wanda ake kira Ma’a Jamamare. Saboda haka ba mu yi mamaki ganin Halilu ya zama ɗan bindiga ba.” Cewar wata majiya.
“Halilu ya fara da satar dabbobin irin su tumaki da awaki, lokacin ya na matashi, har da shanu. Daga nan ya riƙa ya koma fashi da safarar muggan makamai.
Ya haɗu da wani gogarman safarar muggan makamai mai suna Shehu Rekep, wanda ya dawo ƙarƙashin Halilu su na harƙallar shigo da muggan makamai daga Jamhuriyar Nijar,” cewar wata majiya.
Ya yi ƙarfi sosai, domin baya ga sayar da bindigogi, Halilu ya na bayar da hayar bindigogi ga ‘yan bindiga a yankin da ya ke da iko, irin su Maradun, Shinkafi, Kaura Namoda, Zurmi, Bakura, Isa da Sabon Birni.
Shi ne ya horas da Bello Turji, Lauwali Dodo, Ali Ɗan Oga, Chimo da Haru da sauran wasu da dama.
An haƙƙaƙe cewa akwai ‘yan bindiga sun kai 1,000 a ƙarƙashin sa.
Halilu Sububu na da mata uku da ‘ya’ya da dama. Ya tara bindigogi da babura da dama a gidan sa na Sububu da Ruɗani. Kuma ya na da ɗaruruwan shanu.
PREMIUM TIMES ta tattauna da makusantan Halilu Sububu da wasu mutum kusan goma da suka taɓa yi masa aikin bautar haƙo masa ma’adinai.
Discussion about this post