Tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu ya yabi salon mulkin gwamnan Kaduna, Babangida Aliyu bisa yadda ya rungumi kowa sannan yana ragargaza ayyuka a jihar Kaduna ba tare da muzguna wa talakawa ba.
Aliyu ya jagoranci mambobin gidauniyar tunawa da Sardauna zuwa fadar gwamnatin Kaduna domin jajantawa wa gwamnatin rashin mutane masu Maulidi da aka yi a harin tsautsayi na jirgin sama da yayi musu ruwan bamabamai bisa Kuskuri a Kauyen Tudun Biri.
Aliyu ya ce sun kawo ziyara Kaduna ne domin jajanta wa gwamnan da mutanen jihar, kan abin da ya faru a kauyen Tudun Biri.
Sannan kuma Aliyu ya mika godiyarsa ga gwamnan bisa kyautar katafaren fili da ya baiwa kungiyar Arewa, wanda ayyukan duk sun shafi gidauniyar Saudauna.
A jawabinsa, Gwamna Uba Sani ya bayyana matukar jin dadinsa da irin namijin kokarin da gidauniyar tunawa da Sardauna ta yi musamman a fannin ilimi mai matukar muhimmanci. Ya ja hankulan su kan yadda ake fama da matsalar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Arewa, ya kuma jaddada jajircewar gwamnonin Arewa na ganin an shawo kan wannan matsala da kuma kokarin rage jahilci a yankin.
Tun bayan hatsarin bamabamai da aka yi a kauyen Tudun Biri, yan Anjeriya da dama ke kawo ziyara ga gwamnatin Kaduna domin yi wa gwamnati da mutanen jihar Jajen wannan ibtila’i da ya auku ga mutanen jihar.
Discussion about this post