Gwamnatin Najeriya za ta raba Hukumar Bada Wutar ta Ƙasa gida biyu.
A wata sanarwar da aka nuna alamun yin haka, TCN, wato ‘Transmission Company of Najeriya, za a raba shi zuwa gida biyu.
Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke magana a taron Sanin Makamar Aiki na Ma’aikatar sa, wanda ya gudana a ranar Talata, a Abuja.
Kamfanin TCN wanda shi ke tafiyar da aikin raba wuta, ya na ɗaya daga cikin kamfanoni 18 da aka samar daga kamfanin samar da wutar lantarki na PHCN cikin Afrilu, 2004.
TCN ya zama cikakken kamfani cikin Nuwamba, 2005 kuma a cikin shekarar ce aka ba shi lasisin amincewa ya samarwa da raba wutar lantarki.
Kamfanin dai a zaman yanzu mallakin Gwamnatin Tarayya ne.
Adelabu ya ce za a yi wa TCN garambawul, inda za a raba shi gida biyu, wato ISO, mai zaman kan sa da kuma TSP.
Ya ce, “tilas ne mu yi nazarin shin gwamnati ce za ta samar da wuta a ƙasa baki ɗaya, ko kuwa dai kawai damar samar da wuta a ƙasa baki ɗaya za ta bayar.
Ya yi maganar cewa hakan zai bunƙasa samun hasken lantarki a yankunan karkara da kuma faɗin ƙasar nan.
Najeriya na fama da matsalar wutar fiye da shekaru 30. Wannan kuwa ya haifar da ambaliyar janareto-janareto manya da ƙanana, da kuma yawan amfani da hasken rana domin a samun hasken sola.
Haka kuma matsalar ƙarancin wutar lantarki ya haifar da tsadar rayuwa, saboda yawancin ababen da masana’antu manya da ƙananan ke sarrafawa duk san yi tsada.
A cikin 2023, tashar samar da wutar lantarkin Najeriya ta durƙushe sau shida.
Discussion about this post