Wani mutum mai shekaru 31 ya kashe kansa a jihar Abia, a kudu maso gabashin Najeriya, bayan da aka ce ya yi asarar Naira miliyan 2.5 a cacar yanar gizo.
Mutumin mai suna Chukwuma Onoh, an ce ya ciyo bashin Naira miliyan 1.2 daga hannun abokansa inda ya hada da na sa Naira miliyan 1.3 don yin buga cacan amma bai ci ba.
” Zaɓin da ya rage min shine kawai in kashe kaina domin ba zan iya muamula cikin jama’a ba bayan irin wannan abin kunya da ya same ni, sannan kuma ta ina zan samu kuɗin biyan bashin da na ci na buga wannan caca.” Wannan shine saƙon da muka gani wanda mutumin ya saka a WhatsApp.
Matashin ya rika rubuta wa a shafin sa ta Facebook cewa shi zai kashe kansa saboda ya gaji da rayuwar duniya sannan bai san ta inda zai fara neman kuɗi ya biya masu bashi ba.
Ko da ya je siyan maganin kashe kwari ‘Sniper’ sai da ya rubuta a Facebook cewa ” Ga ni nan zan siya maganin kashe kwari zan sha in koma ga mahalicci na. Ba zan iya jure wa wannan hasara da na yi ba.
Ko da abokanan sa suka yi kokarin cimma sa, sun iske ya kwankwaɗi ruwan maganin kashe Kwari har ya fara shureshure.
Likitoci a asibiti sun tabbatar da ya sheka lahira, a lokacin da suke kokarin ceto sa.
Discussion about this post