Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, mallakar Gwamnantin Tarayya (NBS), ta ce malejin tsadar rayuwa ya cilla sama, sosai inda ya yi gwauron tashi zuwa kashi 28.20 a cikin Nuwamba, daga kashi 27.33.
NBS ta bayyana haka a ranar Juma’a, inda Ofishin NBC ya ce tsadar kayan abinci da kayan tsadar rayuwa a cikin Nuwamba, ya ƙaru da kashi 0.87, idan aka kwatanta da watan Oktoba, 2023.
NBS ta ce an samu ƙarin tsadar rayuwa har zuwa kashi 6.73 da idan aka auna watan Nuwamba na 2022 da kuma Nuwamba, 2023.
A shekarar 2022 dai gejin malejin tsadar rayuwa a cikin Nuwamba ya na kashi 22.5
48 ne.
Tuni dai an Najeriya ke ci gaba da shan sukan halin ƙuncin rayuka, tun bayan cire tallafin fetur da kuma sauran dalilai da dama.
Kayan abincin da ake nomawa cikin gida da kuma kayan masarufi sun yi tsadar da da yawan jama’a ba su iya saye ballantana su yi amfani da su.
Sukari da a shekarar da ta gabata ake sayarwa N1,800, yanzu ya kai N4,500.
Discussion about this post