ECOWAS ta amince da sake kafa kwamitin da zai ƙara tattaunawa da Sojojin Mulkin Jamhuriyar Nijar.
A ranar Lahadi ce Shugabannin Ƙasashen da ke ƙungiyar ECOWAS suka amince da sake kafa wani kwamiti da zai sabunta tattaunawa da mahukuntan sojojin mulkin Nijar.
Wannan kwamiti ne zai kasance kwamiti na uku da ECOWAS ta kafa, domin tattaunawa da sojojin mulkin Nijar, waɗanda suka kifar da gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Mohammed Bazoum a ƙarshen watan Yuli.
Har yanzu dai ECOWAS ta na kira da ambato da kuma rubuta wa Bazoum muƙamin sa na ‘Shugaban Ƙasa’, wanda hakan na nufin gwamnatin Sojojin Mulkin Nijar, haramtacciya ce kuma ECOWAS ɗin ba ta amince da ita ba.
Wannan sabon kwamiti ya ƙunshi shugabannin Togo, Saliyo da na Jamhuriyar Benin.
Za su yi ƙoƙarin ganin lallai sun samu tabbaci daga bakin Sojojin Mulkin Nijar cewa za su maida ƙasar ga mulkin dimokraɗiyya nan ba da daɗewa ba, kuma ana buƙatar su gaggauta sakin Bazoum, iyalan sa da wasu makusantan sa da ke tsare.
Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray ne ya karanta jawabin matsayar da shugabannin na ECOWAS suka ɗauka bayan kammala taron na su a ranar Lahadi a Abuja.
Tunanin sake kafa kwamitin ya zo ne kwanaki uku bayan Kotun ECOWAS ta yi biris da roƙon da Nijar ta yi a janye mata takunkumi.
Wannan jarida ta buga labarin cewa Kotun Sauraren Ƙorafe-ƙorafe ta Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) da ke Abuja, ta kori ƙara da roƙon da Jamhuriyar Nijar ta shigar, inda ta nemi kotun ta tilasta ECOWAS ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Jamhuriyar Nijar.
An ƙaƙaba wa Nijar takunkumi ne bayan sojoji sun kifar da gwamnatin farar hula ta tsohon shugaban ƙasa Mohammed Bazoum a cikin watan Agusta.
Duk da kotun ta ce ta na da iznin sauraren ƙarar, to amma kuma ta ce ba za ta iya bada umarnin a janye wa Nijar takunkumi ba.
Shugaban kotun, Edward Asante, wanda ya jagoranci alƙalai uku wajen sauraren ƙarar da yanke hukunci, ya ce Sojojin Mulkin Nijar sun kasa shigar da ƙarin bayanan da kotun ta nema a buƙatun da suka bijiro a kotun.
An yi wannan hukunci a ranar Alhamis, a zaman da alƙalan uku suka yi a Kotun ECOWAS da ke Asokoro, Abuja.
Sauran alƙalan sun haɗa Gberi-be Ouattara da kuma Dupe Atoki, duk sun amince ta ƙin cire wa Nijar takunkumi.
A ranar 26 ga Yuli ce Sojojin Nijar a ƙarƙashin Abdourahmane Tchiani suka kifar da gwamnatin Bazoum.
Daga nan take Shugaban ECOWAS, Bola Tinubu na Najeriya ya jagoranci ƙaƙaba wa Nijar takunkumi.
Najeriya ta rufe iyakokin ta da Nijar, kuma ta katse wa Nijar wutar lantarki a baki ɗayan ƙasar.
Dama daga Nijeriya ake bai wa Nijar wuta.
Takunkumin dai ya janyo ƙarin raɗaɗin tsadar rayuwa a Nijar da kuma Arewacin Najeriya, musamman a jihohi bakwai da suka yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Cikin makon da ya gabata ne Sanatocin Arewa suka yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya maida wa Nijar wutar lantarkin da aka katse mata, domin takunkumin ya na shafar harkokin kasuwanci da tattalin arzikin Arewa.
Discussion about this post