Binciken da sabuwar kafar yaɗa labarai ta zamani, Bloomberg ta gudanar, ya tabbatar da cewa Naira ce ta uku a jerin kuɗaɗen da suka fi lalacewar daraja a 2023, a duniya baki ɗaya.
Bloomberg ta fi diddigin binciken kuɗaɗen ƙasashe 151, inda ta fayyace cewa in banda fam na ƙasar Lebanon da Peso na Ajantina, babu kuɗin da ya kai lalacewar daraja kamar Naira ta Najeriya, a cikin 2023.
A ranar Alhamis ɗin ƙarshen Disamba 2023, kwanaki uku kafin ƙarshen shekarar, an sayar da Dalar Amurka 1 kan Naira 1,043 a kasuwar ‘yan canji.
Amma a ranar Juma’a, ta koma Dala 1 kan Naira 907.12, kamar yadda FMDQ ya nuna, sannan zuwa yamma ta ƙara lalacewa, ta koma darajar Naira 1,193 duk Dalar Amurka 1 a farashin gwamnati, a ranar Juma’a.
Yayin da masana tattalin arzikin ƙasa ke hasashen cewa darajar Naira za ta ƙara faɗuwa ƙasa warwas a cikin 2024 mai kamawa tun daga gobe Litinin, Naira ta kasance ta fi shan dukan tsiya a hannun Dala da Fam da Yuro cikin 2023, dukan da ba ta sha irin sa ba tun daga 1999.
Kuɗaɗen ajiyar Najeriya da ke Asusun Ajiyar Ƙasashen Waje sun yi ƙasa sosai, ƙarancin da tun shekara shida baya ba su yi ba.
Wani kamfanin binciken hada-hadar kuɗaɗe mai suna Capital Management Ltd, ya ce darajar Naira za ta ƙara zubewa, sai fa idan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jawo masu zuba jari daga waje, sun narka jari tukunna.
Discussion about this post