Yayin da ‘yan Najeriya suka fara ɗanɗana kaifin kuɗar gatarin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya fara daddatsa masu ƙauri da shi tun a ranar da aka rantsar da shi, jama’a tun daga manya har zuwa na ƙasa an shiga mawuyacin halin da ba a yi tsammani za a shiga ba, dalilin cire tallafin fetur, wanda aka maida sabon farashin lita ɗaya Naira 620.
Wannan raɗaɗin tsadar rayuwar ya buwayi kowa a ƙasar nan, amma dai waɗanda suka fi jin jiki su ne marasa galihu, musamman waɗanda sai sun yi zirga-zirga kafin su samu abin saka wa bakin salati. Nan da nan tsadar fetur ta haifar da tsadar sufuri, ta yadda tilas ta sa ma’aikatan gwamnatin tarayya har ma da jihohi da dama suka riƙa yin fashin zuwa aikin ofis.
Zuwa yanzu abin ya zama jiki a jihohi daban-daban, haka a Babban Birnin Tarayya Abuja. Yawancin ma’aikata sau biyu su ke zuwa aikin ofis a cikin mako ɗaya. Wasu idan su ka je ranar Litinin, suka sake leƙawa a ranar Laraba, to shikenan sai kuma wani satin
Wasu kuma ranakun Laraba su ke zuwa da kuma Juma’a, shikenan sun arce sai kuma wani mako.
Da yawa kuma a halin yanzu kwata-kwata ba su zuwa aikin, amma sun kafa guruf na ma’aikatan da ke ɓangaren su a WhatsApp. Idan akwai wani aiki ya taso wanda ake buƙatar wane da wane su je ofis gobe, to sai a sanar a cikin WhatsApp guruf.
Cire tallafin fetur ya haifar da tsadar sufuri, wanda hakan ya lalata aikin gwamnati a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu. Kuma haka ake tafiya, domin kowace ma’aikata minista ya san abin da ke faruwa, amma ya kauda kai. Haka shugabannin kowace hukuma ko cibiya ya san ma’aikatan sa sun daina zuwa aiki kowane rana daga Litinin zuwa Juma’a, amma ya kauda kai.
Discussion about this post