Ɗan Majalisar Tarayya Yusuf Gagdi daga Jihar Filato, ya shiga tsomomuwa bayan ya yi bugun ƙirjin cewa jam’iyyar APC a Filato za ta iya murɗe shari’ar zaɓen gwamnan jihar a Kotun Ƙoli.
An nuno shi a cikin wani bidiyo wanda aka watsa a soshiyal midiya, inda Gagdi ɗin ke tinƙaho da bugun ƙirji a wurin wani taro a Filato, a ranar Lahadi, ya na nuna cewa APC za ta iya murɗe shari’ar domin ta samu nasara a Kotun Ƙoli.
A ranar Lahadi ce dai Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓen Gwamna Celeb Mutfwang na PDP a Jihar Filato, ta ce ɗan takarar APC, Nentawe Goshwe be ya yi nasarar zaɓen gwamnan.
Shugaban Riƙo na PDP, Umar Damagum ya nemi a sake bin diddigin yadda aka zartas da hukuncin, tare da cewa an yi son kai.
Gagdi, ɗan majalisa mai wakiltar Pankshin/Kanam/Kanke, a ƙarƙashin APC, ya ce sakamakon shari’ar da za a yi a Kotun Ƙoli, zai ta’allaƙa ne ga jam’iyyar da ta fi kusanci ga alƙalan kotun.
“Mun je Kotun Ɗaukaka Ƙara, saura Kotun Ƙoli, inda za mu haɗu a can. To a can ne za mu san waɗanda suka sani, kuma su ma za su san waɗanda muka sani”, haka ya furta a cikin bidiyon mai sekan 18.
Gagdi dai tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Filato ne, kuma wannan ne zangon sa na biyu a Majalisar Tarayya.
Ya yi takarar zama Kakakin Majalisar Tarayya, amma bai samu ba. Sai aka naɗa Tajuddeen Abbas daga Jihar Kaduna.
Ana zargin sa da karɓar toshiyar baki a Kwamitin Binciken Harƙallar Ɗaukar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
Tuni Najeriya aka ruɗe wajen caccakar Gagdi a soshiyal midiya.
Dama kuma ana caccakar yadda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓen Kano, kuma ta ayyana na Jihar Zamfara a bai kammalu ba.
Jihohin uku, Kano, Zamfara da Filato dai duk a hannun jam’iyyun adawa suke.
Discussion about this post