An tsamo gawar wani Arɗon Fulani mai suna Arɗo Umar Ibrahim, wanda aka neme shi aka rasa a ranar Laraba.
Marigayin wanda kuma shi ne Ciroman Fulanin Kumbun da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mangu a Jihar Filato, an tsinci gawar sa ce a cikin wata tsohuwar rijiya a garin Jokom, wanda gari ne na ƙabilun Mangu masu faɗa da Fulani makiyaya.
Kakakin Sojojin Operation Safe Haven, Oya James, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Litinin.
Mamacin wanda shi ne Ciroman Fulanin Kumbun da ke yankin Mangu, an neme shi ba a gani ba a ranar Juma’a, bayan ya fita daga asibiti, da niyya zai je ya sayo abinci ya kai wa matar sa, wadda aka kwantar asibitin.
Haka dai Shugaban Ƙungiyar ‘Gam Allah Fulani Development Association of Nigeria, (GAFDAN) ys shaida wa Daily Trust.
“Bayan an shafe kwanaki huɗu ana nema da cigiya, sai aka samu gawar sa cikin wata tsohuwar rijiya, wadda ba wata tazara mai nisa tsakanin rijiyar da asibitin da aka kwantar da matar tasa.
“Sojojin Operation Safe Haven ne su ka tsamo gawar, kasancewa su ne ke samar da tsaro a yankin.”
Wannan lamari ya faru watanni biyu bayan kisan wani Arɗon Fulani, Adamu Idris a dai cikin ƙaramar hukumar Mangu ɗin.
PREMIUM TIMES Sojoji sun damƙe makashin Arɗon Fulanin Filato, a maɓuyar sa, a Legas
Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa zaratan sojojin ta na ‘Kowa Ya Kwana Lafiya Shi Ya So’, wato ‘Operation Safe Haven’, sun samu nasarar damƙe Philip Gokas, wanda aka fi sani da Jaykimo a Lagos, bayan sun shafi makonni su na farautar sa.
Ana zargin sa da kisan Arɗon Fulanin Panyam a Ƙaramar Hukumar Mangu, Jihar Filato.
A ranar 24 ga Satumba ce dai aka nemi Arɗo Idris aka rasa, lokacin da ya ke kan hanyar sa ta komawa gida, bayan ya je ta’aziyya a Mangu.
Daga baya an tsinci gawar sa a cikin wani ramin da aka rufe shi a cikin dajin jihar Bauchi mai maƙwautaka da Filato.
Idris ya koma Bauchi bayan da rikicin Fulani da ƙabilun Mangu ya kai ga an yi wa Fulani munmunan kisa, har aka ƙone rugagen su, tsakanin su da ƙabilar Mwaghavuls da ke yankin Mangu.
Rikicin dai ya ci rayukan ɗaruruwan mutane, kuma dubban mutane sun rasa muhallin su.
Kakakin Rundunar OPSH, Oya James, ya ce zaratan sojojin su sun samu galabar damƙe wanda ake zargin a wani gidan kallon ƙwallo, cikin unguwar Ogba a jihar Legas.
“Gokas ya furta da bakin sa cewa shi ne ya kashe Arɗon Fulani Idris, kuma ya yi ƙarin hasken yadda za a iya kamo wasu da ke da hannu wajen kisan, nan da ‘yan kwanaki kaɗan.
“Idan ba a manta ba, tun lokacin da aka kashe Arɗon Fulanin, Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Taoreed Lagbaja ya bada umarnin cewa lallai a tabbatar da an kamo masu hannu a kisan, kafin nan kuma ya bada umarnin a gano gawar mamacin, kuma duk aka yi hakan a cikin dajin Bauchi. An gano gawar sa, kuma aka damƙa ta ga iyalan sa, suka sallace ta.”
Discussion about this post