Gwamnan Kaduna Uba Sani ya bayyana jin dadinsa a lokacin da ya samu labarin sakin dalibin makaranta Bethel da ‘yan bindiga suka saki bayan ya shafe kwanaki sama da 800 tsare hannun ‘yan bindigan.
Idan ba a manta ba tun a shekarar 2021 ne yan bindiga suka sace daliban makarantyar Bethel dake Kaduna. Maharan sun kwashe dalibai 121 suka yi awon gaba da su.
Bayan haka ne iyaye da yan-uwa suka rika tara kudi suna biyan maharan domin su saki yayan su. Kadan da kadan dai haka aka rika dankara wa maharan miliyoyin naira suna sakin yaran makarantar.
Maharan sun saki duka daliban saura daya tal, wato Ayuba.
A ranar Alhamis, suka sake shi ya dawo ga iyayen sa.
Bayan haka ne kakakin gwamnan jihar Mohammed Shehu ya fidda sanarwar nuna farin cikin gwamna Sani ga hakan.
” Gwamna Uba Sani ya nuna farincikinsa ga sakin wannan dalibi da yan bindiga suka yi. Ina mai fatan irin haka ba zai sake faruwa ba a jihar.
Sannan kuma gwamna Sani ya yai alkawarin cigaba da tsananta tsaro a fadin jihar ta hanyar ganin an kawo karshen hareharen yan bindiga a ko ina a fadin jihar.
Discussion about this post