Kungiyar malaman koyar da aikin kiwon lafiya dake babban asibitin Ilorin Jihar Kwara SHEPAN ta bayyana cewa mutum 590,000 ne ke kamuwa da tarin fuka duk shekara a Najeriya.
Farfesa Sunday Aderibigbe ya sanar da haka ranar Talata a taron tattauna hanyoyin inganta fannin kiwon lafiya da kungiyar ta shirya kuma aka yi a garin Ilorin.
Aderibigbe ya ce zuwa yanzu cutar na kashe mutum kashi 10% a Najeriya duk shekara.
Ya ce hakan na da nasaba da yadda gwamnati ta kasa inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.
Aderibigbe ya yi kira ga gwamnati da ta kirkiro kudirorin da za su taimaka wajen inganta fannin lafiyar kasar nan domin inganta lafiyar mutanen Najeriya.
Tarin fuka cuta ce dake kama huhun mutum inda kwayoyin cuta na Mycobacterium tuberculosis ke haddasa cutar a jikin mutum.
Sakamakon bincike ya nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashe 30 da cutar ta yi tsanani a cikinta a duniya sannan na daya a daga cikin jerin kasashen Afrika da suka fi samun mutanen dake dauke da cutar ba tare da gwamnati ta san da zaman su ba.
Yin allurar rigakafi na daga cikin hanyoyin samar da kariya daga kamuwa da cutar amma wani sakamakon bincike da kungiyar lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya nuna cewa cutar na kisan mutum 245,000 sannan wasu mutum 590,000 na kamuwa da cutar a duk shekara.
Kuma dai cikin mutum 590,000 dake kamuwa da cutar mutum 140,000 na dauke da cutar kanjamau kuma.
Discussion about this post