Wani manomin shinkafa mai suna Clever Amada da ke Jihar Bayelsa ba shi da wata dabara ko hikimar cashe shinkafar da ya noma, har sai ya loda ta ya kai Jihar Delta ko Ebonyi, inda a can ne kaɗai zai iya samun injin casar shinkafa na ‘yan kasuwa.
Da a ce wani shirin karɓo ramcen dala miliyan 326 daga Chana ya tabbata, wanda Gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta yi alƙawari tun a 2016 ya tabbata, to zai iya kasancewa an yi amfani da kuɗin an kafa masana’antun casar shinkafa har guda 40.
Amma shirin sai ya shiririce, saboda Exim Bank na Chana ya ƙi bayar da kuɗaɗen.
“A Jihar Bayelsa ba mu da takamaimen masana’antar casar shinkafa.” Haka Amada ya bayyana wa PREMIUM TIMES. Kuma shi ne Sakataren Ƙungiyar Manoman Shinkafa na Jihar Bayelsa.
“Kamar yadda babu a Bayelsa, haka babu a Ribas da Akwa Ibom. Kuma ba na jin ko a Jihar Cross River akwai ko guda ɗaya. Don haka gaba ɗayan Kudu maso Kudu, babu wani gangariyan masana’antar tace shinkafa ko guda ɗaya.”
Ire-iren su Amada na da yawa a yankin, kuma duk irin matsaloli ɗaya su ke fuskanta a Kudu maso Kudu.
China dai ita ce ta fi bai wa ƙasashen Afrika bashi tsawon shekaru 20 baya zuwa yau.
Najeriya kaɗai ta kinkimo bashin dala biliyan 4.29 daga Chana, idan aka yi la’akari da ƙididdigar watan Disamba, 2022 ta nuna kuma ta tabbatar.
Sai dai kuma kuma daya shekaru uku da suka gabata zuwa yanzu, masu bada lamuni daga Chana sun rage bayarwa sosai ga ƙasashen Afrika, ciki har da Najeriya.
Dalili kenan rashin bayar da lamunin ya riƙa kawo naƙasu a ayyukan raya ƙasa daban-daban, cikin kuwa har da shirin noma a Najeriya da wasu ƙasashen Afrika.”
Haka Anietie Umoren ya bayyana. Shi ne babban jami’in bincike a Ƙungiyar ‘No Hunger Food Bank’, wadda ke kula da bayar da agaji.
Tulin Ayyukan Da Aka Fara Aka Watsar, Saboda Chana Ta Ƙi Bayar Da Kuɗi:
Ba a ɓangaren aikin noman shinkafa kaɗai ba ne aka yi watsi da manyan ayyukan raya ƙasa, sanadiyyar ƙin bayar da lamunin maƙudan kuɗaɗen da Chana ta yi a Najeriya.
Chana ta ƙi bayar da kuɗaɗe har dala biliyan 5.3 domin aikin titin jirgin ƙasa daga Ibadan zuwa Kano. Kuma ta ƙi bayar da lamunin Dala biliyan 3 domin gina titin jirgin ƙasa mai tsawon kilomita 1,000 daga daga Fatakwal zuwa Maiduguri.
A ɓangaren aikin titin jirgin ƙasa daga Ibadan zuwa Kano, Gwamnantin Tarayya ta bayar da kashi kashi 15 bisa 100 na kuɗin. Haka can ma a ɓangaren aikin titin jirgin ƙasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri, an bayar da kashi 15 bisa 100. Amma rashin samun kashi 85 daga Chana, ya kasance aikin ba zai yiwu ba, sai fa idan ita gwamnatin ce za ta iya kamfatar maƙudan kuɗaɗe ta yi aikin, ko kuma ta tafi wata ƙasar ta sake kinkimo wani bashin.
Aiki dai an fara, domin kamfanin CCECC na Chana ya fara shimfiɗa layin dogo. Amma kuma babu kashi 85 na uwar kuɗin da za a ci gaba da aiki.
Wannan bayani na sama, tsohon Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana shi, yi a cikin 2022.
Haka aikin titin jirgin ƙasa na cikin Abuja, shi ma ya kakare, saboda Chana ta ƙi sakin kuɗi har dala miliyan 157 da ta yi alƙawari.
Haka Bankin China Exim Bank ya ƙi bayar da dala miliyan 183.62 da dala miliyan 208.90 domin faɗaɗa filayen jiragen sama huɗu a Najeriya. Tun cikin Disamba 2021 aka yi yarjejeniyar, amma har yau Chaina na ƙi sakin kuɗaɗen. Haka dai Hukumar Kula da Basussuka ta Ƙasa (DMO) ta tabbatar.
Tuni dai an faɗaɗa aikin filayen jiragen da wani bashin na dala miliyan 500 daga Chana, da kuma dala miliyan 100 daga gwamnatin Najeriya.
Amma kuma filayen jiragen saman Abuja da na Legas na buƙatar gagarimin aiki da kwaskwarima da garambawul ɗin kayan aiki da cire wasu a musanya su da sabbi, amma abin ya gagara.
Tsohon Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika cewa ya yi irin yadda aka tsara ginin filayen tun daga farko, ba zai yiwu a iya yi masu sabbin gyare-gyaren da su ke buƙata a yanzu ba.
Masana sun ce Chana ta ja baya daga bai wa Najeriya basussuka, saboda ta na ganin akwai kasada sosai ta riƙa zuba kuɗaɗen ta a fannonin ayyukan da babu garanti ɗin samun riba.
Sannan kuma ɓarkewar cutar korona da yaƙin Ukraniya da Rasha, ya kawo cikas wajen riƙa bayar da lamuni.
Yayin da ayyukan da aka fara suka tsaya cak bayan Chana ta ƙi bayar da kuɗaɗe, al’ummomin da aka fara ayyukan a yankunan su sun fara kokawa cewa rayuwar su na cikin tsaka-mai-wuya.
Har a yankin Abuja manoma shinkafa na fuskantar irin matsalar da manoman shinkafar Kudu maso Kudu ke fuskanta, wato rashin gangariyar wurin casar shinkafa. Tun daga yankin Angwa har zuwa manoman da ke Gwagwa duk matsalar iri ɗaya ce a yankin Abuja.” Haka wata mata mai suna Comfort Sunday ta shaida wa wakilin mu.
Binciken PREMIUM TIMES ya nuna a yanzu ana sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 kan Naira 50,000.
Discussion about this post