Jam’iyyar PDP a Kaduna ta bayyana ce wa ficewar tsohon gwamnan jihar Ramalan Yero daga jam’iyyar bai ɗaɗa ta da kasa ba ko kaɗan.
Shugaban jam’iyyar Felix Hyet ya bayyana haka a hira da ya yi da Kamfanin dillancin labaran Najeriya a Abuja ranar Lahadi.
Hyet ya ce dama Yero ba shi da wani tasiri a jam’iyyar PDP kuma.
” Ruwa ne ya ƙare wa ɗan kada, amma tuni Yero ya zama fanko, a PDP, babu shi tasiri kuma ba magoya baya. Ta kare masa. Ficewar sa ko a ƙumbar mu.
Hyet ya kara da cewa jam’iyyar PDP ba za ta yi kewar Yero ba don sama can babu abinda ya ke tsinana wa PDP a jigae da kasa baki ɗaya.
Idan ba a manta ba, a makon jiya, Yero ya sanar da ficewarsa daga PDP, inda ya mika katin shaidar zama ɗan jam’iyya a gundumarsa a Zaria.
Har yanzu Yero bai faɗi ko wata jam’iyya ya tsunduma ciki ba.
Ba Yero bane kawai ya fice daga PDP a cikin shima ɗan majalisa Godfrey Gaiya wanda tsohon ɗan majalisa ne ya sauya sheka zuwa APC.
” A yadda nuka ji, wai an yi wa Gaiya alƙawarin kujerar minista amma kuma ga dukkan alamu dai maganar ta bi ruwa domin an naɗa minista saga Kaduna.
Discussion about this post