Gwamnan Kaduna Uba Sani, ya naɗa Abdulƙadir Mayere a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar.
Mohammed Shehu, Kakakin gwamna Sani ya sanar da haka a wata takarda da ya fidda ranar Litinin.
Shehu ya ce gwamna Sani ya amince da naɗin Mayere a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Kaduna wanda soma aiki nan take.
Mayere ya rike muƙaman babban sakatare a wasu manyan ma’aikatun gwamnatin tarayya kafin ya yi murabus.
Mayere zai maye gurbin Balarabe Lawal Wanda shugaban kasa Bola Tinubu ya naɗa
Ministan Muhalli.
Discussion about this post