Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarnin a biya malaman jami’o’i albashin su na watanni takwas da gwamnatin Buhari ta riƙe masu lokacin yajin aikin game-garin Jami’o’in Najeriya baki ɗaya.
Tinubu ya bada wannan umarnin ne a ranar Juma’a, shekara ɗaya cif bayan janye yajin aikin da malaman jami’o’in suka shafe watanni takwas su na yi.
Wannan umarni na ƙunshe a cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a.
Sai dai kuma gwamnatin ba ta ce komai ba dangane da albashin sauran ƙungiyoyin cikin jami’o’i da suka taya malaman jami’o’i, wato ASUU yajin aiki.
Kakar yadda Ngelale ya bayyana a cikin sanarwar, ya ce Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon sa na Shugaban Ƙasa, ya yi wa malaman jami’o’i afuwa, ta hanyar cire masu dokar ‘Ba Albashi Ga Wanda Bai Je Aiki Ba’, wadda aka ƙaƙaba wa ma’aikata, a zamanin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari kan Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), tsawon watanni takwas da suka yi su na yajin aiki, daga 14 ga Fabrairu, 2022 har zuwa Oktoba, 2022.
“A ƙoƙarin sa na sauƙaƙe wa jama’a matsin rayuwar da suka shiga, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarnin a biya malaman jami’o’i dukkan albashin watanni takwas da su ke bi. Hakan zai ba su damar karɓar albashin watanni huɗu, a yanzu kamar yadda aka yi jarjejeniya da su.
Lokacin da ASUU ta tafi yajin aiki, gwamnatin tarayya ta yi amfani da Sashe na 43(1)(a), ta ƙaƙaba masu dokar ‘no work, no pay”.
Sai dai kuma Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i ta Ƙasa, SSANU, ta yi barazanar cewa ita ma ko dai a biya mambobin ta na su albashin na watanni huɗun tare da malaman jami’o’i, ko kuma su sake tafiyawani sabon yajin aikin a yanzu.
Haka dai Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Abdussobur Salaam ya shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Juma’a.
Discussion about this post