Mazaunan Babban Birnin Tarayya Abuja sun kai kukan su ga gwamnatin tarayya da ta saka baki a tsawalla kudin haya da masu gidaje yi a Abuja.
Wani Dauda Abusali dake sana’ar zane ya ce a dalilin kara kudin haya da mai gidan da yake zamam ciki ya yi ya sa ba zai iya biya ba dole ya koma zama da abokinsa a daki daya.
“Mai gidan da nake haya ciki ya ce duk Wanda ba zai iya biyan sabon kudin hayan gidan ba ya tashi. Na tura iyalina su koma gida ni Kuma Ina nan Ina neman kudi.
Abusali ya ce akwai gidaje da dama a Abuja da ba a zama a ciki saboda tsadan kudin haya.
“Ina kira ga gwamnati da ta kirkiro hanyoyin da zai sa a rage kudin haya a babban birnin tarayyar.
Wani mai gidan haya Banji Oluwaseyeri ya ce gidajen haya na tsada a Abuja saboda tsadar rayuwar a garin.
Oluwaseyeri ya ce abinci da kudin mota duk sun karu. Dole suma su kara kudin hayan.
NAN ta ruwaito cewa kudirin neman hana masu gidajen haya a Abuja karban adibans din shekara daya duk shekara ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa ta 9.
Dokar mai taken, “Kudirin doka domin tsara yanayin biyan kudin haya a Abuja.
Kudirin da Smart Adeyemi (APC Kogi-West) ya dauki nauyinsa, an yi shi ne domin kawo karshen yadda masu gidajen haya ke naman a biya su adibans na shekara daya kuma duk shekara.
Discussion about this post