Hukumar kula da al’amuran mata da raya al’umma tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan jihar Anambra sun kama wata mata Oluchukwu Nwosu bisa laifin siyar da jikanta dan wata uku akan naira 50,000.
Oluchukwu ta siyar da jaririn ba tare da ta sanar da mahaifiyar yaron ba Ijeoma wacce ta haihu ba tare da ta yi aure ba.
Maitaimakawa kwamishinan kula da al’amuran mata da raya al’umma ta jihar kan harkokin yada labarai Chidinma Ikeanyionwu ta sanar da haka a wata takarda da manema labarai suka samu ranar Lahadi.
Ikeanyionwu ta ce hukumar ta ceto wannan jariri bayan mahaifiyarta Ijeoma ta kawo kara ofishin su.
“Mun ceto jaririn bayan mun dauki kusan wata daya muna gudanar da bincike inda tare da hadin gwiwar ‘yan sanda muka kamo mutanen dake cikin hada-hadar siyar da jaririn.
Wahala ce ta sa na siyar da jika ta – Oluchukwu
Kakan jaririn Oluchukwu bayan ta shiga hannun jami’an tsaro ta ce ta siyar da jaririn ne saboda wahala da rashin kudin kula da shi.
“Haihuwar ‘yata Ijeoma uku kenan ba a aure ba kuma tun da ta fara haihuwa cin abinci ke mana wahala. Muna cikin tsananin talauci.
An karbi yara biyu din da Ijeoma ta haifa kafin wannan jaririn sannan zuwa yanzu suna zama a gidan marayu.
Ta ce ta amince ta siyar da jaririn bayan wani Tochukwu Asiegbu ya yi mata tayin cewa zai siya jaririn komai tsadarsa.
Asiegbu ya ce ya ci ribar naira 30,000 da ya kara awajen siyar da jaririn.
Ma’aikatar ta ceto jaririn daga hannun wata mata Evelyn Egwuatu wacce ta ce ta biya wata Ebelechukwu Uba naira 200,000 domin ta kawo mata jariri.
A takaice dai Evelyn, Ebelechukwu, Asiegbu da Oluchukwu sun ce hada-hadar siyar da jaririn ya faru a cikin wata uku.
Discussion about this post