Shugaban hukumar dakile yaduwar cutar Kanjamau ta kasa NACA Gambo Aliyu ya ce inganta yin gwajin cutar, inganta bada magani da kula na daga cikin matakan da za su taimaka wa Najeriya wajen cimma burin UN na kawar da cutar nan da 2030.
Aliyu ya fadi haka ne a taron kwanaki biyu da ya yi da manema labarai da masu kwazo a shafukan yanar gizo a Abuja ranar Alhamis.
Yakin dakile yaduwar kanjamau yaki ne da aka dade ana fama da shi inda a yanzu ya kamata mutane su gane cewa suna da mahimmiyar rawan da za su iya takawa a yakin.
Zuwa yanzu dai babu maganin cutar amma akwai magungunan dake hana cutar tasiri a jikin mutum inda haka ke hana cutar kisan mutane.
“Yanzu mun kai matsayin da idan mutum na dauke da kwayoyin cutar zai iya zuwa asibiti domin samun magani kyauta. Yin haka hanya ce dake taimakawa wajen dakile yaduwar cutar.
“Muna so mutane su rika zuwa asibitoci da kansu domin yin gwajin cutar ko karbar magani ba sai mun bi su ba.
“Yanzu akwai mutane da dama dake dauke da cutar Kuma suke rayuwa cikin koshin lafiya. Da dama daga cikin wadanda ke dauke da cutar dake rayuwar su cikin koshin lafiya masu shekaru 34 zuwa 49.
Aliyu ya ce NACA ta yi amfani da mutane daban-daban wajen wayar da kan mutane game da cutar.
Toyin Aderibigbe ta ce kafafen sada zumunta na yanar gizo dandali ne da zai taimaka wajen wayar da kan matasa yaduwar cutar sannan da wayar da kan mutane illan nuna wa masu fama da cutar wariya.
Discussion about this post