A jihar Ribas, an barke da tashin hankali da ruɗani ma tsanani a majalisar jihar, yayin da ƴan majalisa suka yi kokarin tsige gwamnan jihar.
Sashe guda na majalisar ne ya rushe sanadiyar tashin nakiya wato bom.
Jihar ta afka cikin tsaka mai wuya sanadiyyar saɓani da ake zaton ya shiga tsakanin tsohon gwamnan jihar, Nysom Wike da gwamnan jihar Siminalayi Fubara.
Har yanzu minista Wike bai ce komai game da rikicin.
Gwamna Fubara, ya zargi ƴan sandan da kai masa farmaki da gangar, ya ce sun buɗe masa wuta, tare da harba masa ɓarkonun tsohuwa a tawagarsa a Fatakwal.
Bayan haka sai aka rika bugawa a shafukan sada zumunta a yanar gizo, cewa gwamnan ya kori duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar, da wasu jami’an gwamnati wanda Wike ya naɗa kafin ya tafi.
Sai dai kuma kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Warisenibo Johnson, ya karyata wannan batu, yana mai cewa shugabannin kananan hukumomin duka na nan daeam suna aikin su.
Gwamna ya ce ” Ba nada shugabannin ƙananan hukumomin aka yi zaɓansu aka yi. Saboda haka sai wa’adin su ya cika a farkon shekarar 2024.
Sannan kuma Johnson ya kara da cewa ko wasu jami’ai da ake zargin wai Fubara ya sallama ƙaeya ne.
” Idan akwai ƙarin bayani da ake so a ji daga fadar gwamnatin jihar, zan mu samar muku kai tsaye.
Discussion about this post