Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce ba ya da wani shiri na sake fasalin Naira.
CBN ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar tare da sanya hannun Daraktan Sadarwa na Bankin, Isa AbdulMumin, wanda aka buga a X (wanda aka fi sani da Twitter) a ranar Talata.
An jawo hankalin Babban Bankin Najeriya (CB) kan yadda aka rika yada sakonnin tes da ke nuni da cewa Bankin na shirin sake canza farashin kudin kasar nan na Naira daga watan Janairun 2024,” in ji sanarwar.
“Mun damu da cewa wannan labari, wanda muka karyata a baya, da alama yana samun karbuwa tare da muhawara da yawa game da tasirin irin wannan manufa ga tattalin arzikin Najeriya.”
Canjin kuɗi irin haka ya ƙunshi canja fasalin kudi da zai canja darajarsa, ta hanyar ko dai a ƙara sifili ɗaya ko biyu a karshe ko kuma a rage sifili.
CBN ya ce a yi watsi da wannan batu, sai dai kuma ya yi ƙarin haske cewa akwai yiwuwar za a samu sauye-sauye masu ma’ana nan ba da dadewa ba, kuma za abi shi kamar yadda doka ce ta gindaya.
Mutane da dama sun rika tofa albarkacin bakunansu game da wannan sako wacce CBN ta ƙaryata.
CBN ya ce wasu ne suka kirkiro wannan sanarwa domin su jirkita tunanin mutane da kawo ruɗani a tsakanin jama’a.
Discussion about this post