Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ku bayin Allah masu girma, masu daraja, ku sani, lallai fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) ya kasance mai tausayine ga al’ummarsa, baya so a kuntata wa bayin Allah, ko a wahalar da su, ko a kirkiro wasu hanyoyin da zasu zama sanadiyyar kuntatar al’ummah.
Saboda muhimmancin shugabanci da muhimmancin shugaba da girman matsayinsa a cikin al’ummah, yasa Annabi (SAW) yayi kira ga shugabanni a ko wane mataki, da suji tsoron Allah, suyi kokari su samo ingantattun hanyoyin da zasu zama sanadiyyar sauki ga wadanda suke shugabanta.
Duk wata hanya da zata cutar da al’ummah, Annabi (SAW) ya hana bin ta.
Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) kamar haka:
عن عائشة رضي الله عنها قَالَتْ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلّى اللهُ عَلَيْهِ وسَلَّم يقُولُ في بيتي هَذَا:
“اللهم من وَلِيَ من أمر أمتي شيئًا فَشَقَّ عليهم، فَاشْقُقْ عليه، ومن وَلِيَ من أمر أمتي شيئًا فَرَفَقَ بهم، فَارْفُقْ به.” [رواه مسلم]
Daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace: Naji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin wannan daki nawa: “Ya Allah, duk wanda aka dora a bisa wani shugabanci na al’ummata, sai ya kuntata masu, ko ya fito da wata hanya da zata zama sanadiyyar kuntatarsu, ya Allah shima ka kuntata masa, kar ka tausaya masa. Sannan ya Allah, duk wanda aka dora akan wani shugabanci na al’ummata, sai ya saukaka masu, ko ya fito da wata hanya da zata zama sanadiyyar samun sauki a gare su, to ya Allah ka saukaka masa, ka tausaya masa.” [Muslim ne ya ruwaito shi]
‘Yan uwana masu daraja, a cikin wannan Hadisi lallai akwai tsoratarwa da kira ga shugabanni a ko wane mataki, da suyi hankali, su kiyaye, kar ya zamanto suna cutar da mabiyansu ta ko wace hanya. Domin lallai ko shakka babu, duk shugaban da yake kuntatawa bayin Allah, to ya sani, shima Allah sai ya kuntata masa, Allah zai rikita al’amarinsa.
Lallai shugabanni a ko wane mataki, su sani, ko kuma wadanda suke kusa dasu, suji tsoron Allah, su sanar dasu gaskiyar irin hadarin dake tattare da kuntatawa bayin Allah wadanda ake shugabanta.
Shugabanni suyi kokari, su fito da wasu tsare-tsare, wadanda zasu zama sanadiyyar saukakawa bayin Allah. Kar ya zamanto suna ayyana tsare-tsaren da zasu zama cutarwa ga bayin Allah. Domin yin haka lallai ko shakka babu, su ma Allah zai iya jefa su cikin halin kunci da damuwa. Kuma wannan zai iya jawo masu rikicewar lamurransu baki daya, a wayi gari sun shiga cikin halin tsanani da damuwa, wadda Allah ne kadai yasan iyakar ta.
Manufar shugabanci shine, a samar wa da al’ummah hanyoyin sauki a cikin dukkanin ko wane bangare na rayuwarsu. Idan ya zamanto bayin Allah suna shan wahala a shugabanci, to lallai ya kamata a duba, kuma a gyara cikin gaggawa, kafin lokaci ya kure.
Tun farkon shigowar gwamnatin nan mutane suka sake shiga cikin wata sabuwar wahala, wadda dama can akwai wahalar, sai ta karu matuka sosai, sanadiyyar wasu tsare-tsaren gwamnati.
Don haka ina kira ga shugabanni, da suji tsoron Allah, suyi kokari, su fito da wasu hanyoyi, wadanda zasu zama sanadiyyar saukaka wa mutane, domin su kaucewa hadarin da ke tattare da waccan addu’a ta Manzon Allah (SAW) ga miyagun shugabanni, masu tsanantawa al’ummominsu.
Annabi dai yayi addu’a, yace ya Allah, duk shugaban da yake tausayin talakawansa shi ma ka tausaya masa. Duk kuma shugaban da baya tausayin talakawansa, shi ma kar ka tausaya masa ya Allah.
Kuma wallahi, addu’ar Manzon Allah (SAW) karbabbiya ce. Annabi yayi addu’a kuma Allah ya amsa ko shakka babu akan hakan.
Don haka ya rage ga duk wani shugaba daga cikin shugabanni. Idan kun tausayawa bayin Allah, ku ma Allah zai tausaya maku. Idan kuma kun kuntatawa bayin Allah, to ku sani, wallahi ku ma Allah zai kuntata maku.
Kuma ku sani, ina mai rantsuwa da Allah, wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, talakawan kasar nan suna cikin kuncin rayuwa matuka. Suna cikin damuwa, yunwa da wahala.
Duk irin misalin da za’a buga maku, na irin wahalar da bayin Allah suke ciki a kasar nan, to an dai fada ne kawai. Amma duk yadda kake tsammani, wallahi wahalar da damuwar sun wuce tunanin duk wani mai tunani.
Don haka, muna kira da a gyara, a gyara, a gyara kafin lokaci ya kure maku!
Saboda wahala da kuncin rayuwa, matasanmu maza suna shiga cikin kungiyoyin mabarnata. Mata kuma suna sayar da mutuncinsu. Don haka ku tausayawa bayin Allah!
Daga karshe, ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya baku ikon gyarawa. Allah ya dafa maku. Allah yayi riko da hannayenku akan aikata abun da yake shine daidai. Allah ya baku ikon fito da tsare-tsaren da zasu zama sanadiyyar kubutar da bayin Allah daga cikin wannan kuncin rayuwa da wahalar da suka samu kan su a ciki, sanadiyyar wasu tsare-tsare na gwamnati. Allah ya baku zukatan tausayi da imani. Allah ya baku ikon tausayawa domin kuma Allah ya tausaya maku.
Ina addu’a da rokon Allah ya zaunar da kasar mu Najeriya lafiya. Allah ya kawar da dukkanin damuwa da tashin hankali a kasar mu, amin summa amin.
Wassalamu alaikum
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lamba kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post