Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja, Nyesom Wike, ya soke lasisin mallakar filaye 165.
Cikin masu filayen da abin ya shafa, har da ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, sai na Kamfanin Simintin BUA, da tsohon Gwamna Liyel Imoke.
Cikin wata sanarwa da Babban Sakataren FCT, Olusade Adesola ya fitar a ranar Alhamis, ya ce Minista ya ƙwace filayen saboda masu su sun ƙi ginawa.
Daga cikin wasu filayen dai mallakar wasu manya ne a ƙasar nan, har da na tsohon Ministan Tsare-tsaren Ƙasa Udo Udoma.
Akwai na tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ufot Ekaette da na marigayi Sam Nda-Isaiah.
Haka kuma akwai filin tsohon Alƙalin Kotun Ƙoli, Niki Tobi, tsohon Antoni Janar na Tarayya, Kanu Agabi da sauran su.
Akwai kuma na tsohon Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Osita Chidoka.
Sannan akwai fuloti mai lamba 335 a Katamfe, na Kamfanin Simintin BUA, sai mai lamba 2217 na Julius Berger da shi ma ɗin ke Katamfe, sai na Kamfanin Honeywell Construction Limited Mai Lamba 653, duk an haɗa an ƙwace su. Su waɗannan filayen a Idu su ke.
Sauran filayen da aka ƙwace su na a manyan unguwanni masu tsada kamar Maitama, Gudu da Wuye inda aka soke lasisin filaye manya 41.
An ƙwace filaye 39 a Katamfe, Wuse 2, Jabi, Utako da Idu zuwa Asokoro.
Hukumar FCT Abuja ta yi amfani da Sashe na 28(5)(a) na Dokar Mallakar Filaye ta 1978 wajen soke lasisin filayen.
Idan ba a manta ba, Wike ya sha nanata cewa ko minista ne kai idan ka yi gini ,ba bisa ƙa’ida ba, to zai rushe shi.
Discussion about this post