Ba karamin tashin hankali bane, iyayen da suka tura ƴaƴan su makaranta, su sami labarin cewa Ƴan ta’adda sun sace musu yara, kuma ba a san inda suka shiga da su ba.
Kuma a bin takaici ne, gannin har yanzu, za a iya shiga cikin Jami’a a sace dalibai, har barayin su tsira, kuma a cikin babban birnin jiha.
Ko shakka babu, akwai ayoyin tambaya da dama game da munafar gwamnatin BAT musamman wajen kawo karshen matsalolin tsaron da suka dade suna addabar wannan kasa.
Gannin yadda wannan gwamnatin ta yi ministoci guda biyu da ga yanki guda, kuma tsoffin gwamnoni a yankin da yafi kowane yanki barazanar tsaro. Kuma dukkanin su ba kwararru ba a harkar.
Kusan a tsarin mulki na shekarun nan, wannan ne karon farko da shugaban kasa ya yi wannan tsarin ga ministocin sa.
A cilin shekaru takwas a kasar nan, babu yankin da rashin tsaro ya fi addaba kamar Arewa Maso Yamman wanna kasa. Jahohi irin su Katsina, Zamfara, Kebbi sumyi asarar daruruwan mutane da biliyoyin kudi a hannun Yan Tadda da Yan fashin daji.
Duk da cewa an dan samu saukin wannan ibtala’i , musamman ma sace mutane don neman kudin fansa, sai gashi mun wayi gari da wannan bala’i a Jami’ar Tarayya ta Gusau.
Samun labarin shigar Yan Ta’adda Jami’ar Tarayya da ke Gusau ba karamin tashin hankali bane, da kuma sanya wa mutanen wannan yankin na Arewa tunanin dawowar masifar rashin tsaro da kuma sace mutane don neman kudin fansa.
Kamar yadda bayanai ke cewa, anyi artabu da jami’an tsaro da wannan Yan ta’adda, amma fa wannan Yan ta’adda sun sace kimanin dalibai 26 da shiga da su cikin daji.
Irin wannan ta’addanci ba kawai yana karewa bane, wajen sata da biyan kudin fansa ba, yana rugurguzawa da dawo da cigaban ilimi baya, da sanya wa al’ummah shakkun kaiwa yayan su makarantu.
Wannan ba karamin kalubale bane ga sabbin ministocin tsaron, wanda wannan ya faru a jahar daya daga cikin ministan.
Tabbas a kwai jan aiki a wajen wannan shugabanni wajen fuskantar wannan matsala, mussamman a matsayin na shugabanin wannan yankin.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post