Fiye da tsawon mako ɗaya kenan dai ɗan canji Abubakar Sambo na ta haƙilon kare ƙima da mutuncin sa da darajar kamfanin sa, wato AMA Business Solutions da ke harkokin canji a Abuja.
A zaman tattaunawar da PREMIUM TIMES, Sambo ya bayyana yadda aka yaudare shi a cikin rashin sani, aka yi amfani da asusun akawun na kamfanin sa, har Shugabannin Jami’o’i su ka riƙa ɗirka wa Kwamitin Binciken Daukar Ma’aikata da Majalisar Tarayya ta kafa, su 39.
Sambo ya shaida wa wannan jarida cewa, babu yadda za a yi ya yi tunanin cewa kuɗaɗen harƙalla ne aka riƙa turawa a cikin akawun ɗin sa.
“Da farko dai Stella ce ta kira ni, ta ce akwai wani kwastoman da ke so zai sayi daloli. Ta ce za ta ba shi lamba ta, zai kira ya yi min ƙarin bayani.
Sai dai abin da Sambo Bai sani ba, shi ne Stella Adoga ta na yi wa Honorabul Oluwale Oke gada-gada, kuma bai san cewa Oke ɗin mai sakandare ɗin LBIS ɗan Majalisar Tarayya ba ne.
“Babu yadda zan taɓa zargin cewa akwai harƙalla a cikin lamarin.” Haka Sambo ya shaida wa wakilin mu, a lokacin da ya ke nuna wa wakilin mu irin kuɗaɗen da Stella ta sha tura masa ya na yi mata canji.
Sambo ya kuma shaida wa wakilin mu yadda Shugaban Jami’ar Jos, Tanko Ishaya ya kira shi, har ya aika masa da akawun ɗin da aka riƙa tura kuɗaɗe.
Sambo ya ce mamaki ya fara kama shi, yayin da ya fara ganin ana turo kuɗaɗe tsilla-tsilla.
Daga nan ya ce ya kira Ishaya ya ce ya fara ganin kuɗi ana turawa da miliyan bi-biyu, maimakon gaba ɗaya.
Sambo ya ce bai damu da yawan yi wa Ishaya tambayoyi ba, saboda a zaton sa kuɗaɗen daga makarantar LBIS su ke. “Kuma a tunani na, na ɗauka shi ma Ishaya ɗin ma’aikatacin makarantar LBIS ne, ban san ashe Shugaban Jami’ar Jos ba ne.”
Sambo ya ce hankalin sa ya tashi a ranar 29 Ga Agusta, lokacin da PREMIUM TIMES ta buga labarin harƙallar, ɗauke da sunan asusun akawun ɗin sa.
Ya ce ya kira Ishaya bai ɗauka ba, ita kuwa Stella ta ce za ta bincika, sannan ta kira shi.
“Sai bayan da na karanta labarin da PREMIUM TIMES ta buga, na garzaya banki ana buga min kwafen shaidar kuɗaɗen da su ka shigo asusun akawun ɗin nawa, sai na ga tabbas daga jami’o’i aka riƙa turo min Naira miliyan bib-biyu.”
Ya ce washegari ranar 30 Ga Agusta, sai ya sake garzayawa Providus Bank, ya ce su maida kuɗaɗen da aka turo masa a kowane asusun da aka turo kuɗaɗen daga kowace jami’a, har jami’o’i 14.
Sambo ya ce tun cikin 2010 ya ke harkar canji, inda ya fara a Sahara Exchange da kuka 313 Bureau De Change, daga nan kuma cikin 2016 sai ya kafa nasa kamfanin, AMA Business Solutions.
Ya ce banda harkar canji ba ya wata sana’a.
Tuni dai ICPC ta sa an kulle asusun akawun ɗin Abubakar Sambo, kuma ta fara bincike.
Discussion about this post