Girgizar-kasa da ta auku a kasar Morocco ta yi sanadiyar rayukan mutum sama da 800 sannan wasu da dama su samu rauni.
Tashar talabijin ta kasar Maroko ta ba da rahoton adadin wadanda suka mutu a ranar Asabar, in ji ma’aikatar harkokin cikin gida. Daga cikin wadanda suka jikkata, 205 na halin rai a hannun Allah.
Larduna shida da suka hada da Al Haouz da Ouarzazate da Marrakesh da Azilal da Chichaoua da kuma Taroudant ne girgizar kasar ta afku, kamar yadda ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta bayyana a wata sanarwa ta gidan talabijin yayin da take kira da a kwantar da hankula.
Mazauna yankin dai sun yi ta gudu a kan tituna saboda fargabar rayuwarsu. Girgizar kasar ta lalata gine-gine, motoci da sauransu.
Discussion about this post