Najeriya ta zo ta uku a jadawalin ƙasashen da aka fi aikata muggan laifukan ta’addanci da kashe-kashe barkatai a duniya, a ƙididdigar 2023, wadda Global Organized Crime Index ta gudanar.
Rahoton ya ce har yanzu Najeriya na ci gaba da fuskantar gagarumin ƙalubalen matsalar rashin tsaro da aikata muggan laifuka.
Bincike ya nuna wa GIATOC cewa yawan aikata laifukan ta’addanci da makamantan hakan ya ƙaru sosai a Najeriya da ɗigo 0.13 idan aka yi la’akari da shekarar da ta gabata.
Najeriya ta samu maki 7.28 daga cikin maki 10, inda hakan ya sa za zo ta shiga a duniya, kuma ta 1 a Afrika.
Ƙasar Dimokraɗiyyar Congo na sama da Najeriya wajen yawan aikata ta’addanci da muggan laifuka. Amma kuma wanda ake yi a Afrika ta Kudu bai kama ƙafar na Najeriya ba.
Idan ba a manta ba, a 2021 dai Najeriya ce ta 5 wajen yawan aikata muggan laifukan ta’addanci da kashe-kashe a duniya.
Ƙasar Myanmar ce ta zo ta ɗaya, sai Colombiya, sai kuma Mexico ta uku.
Discussion about this post