Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa ɓangaren CONUA, ta roƙi Gwamnatin Najeriya ta biya mambobin ta albashin watanni takwas da aka riƙe masu.
An riƙe masu albashin ne a lokacin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ta yi yajin aikin game-gari na tsawon watanni da yawa.
A cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai Ma’aikatar Harkokin Ilmi, Ben Goong ya fitar, ya ce Kodinetan CONUA na Ƙasa, Niyi Sunmonu, ya yi roƙon a lokacin wata ziyara da ya kai wa Ƙaramin Ministan Ilimi, Yusuf Sununu.
Sanarwar ta bayyana cewa Minista Sununu shi ma ya gwamnati ta duba yanayin halin da malaman jami’o’i masu koyarwa da sauran ma’aikatan jami’o’i ke ciki, domin a inganta rayuwar su.
Sununu ya ce halin ƙuncin aka shiga a faɗin ƙasar nan na raɗadin tsadar rayuwa bayan cire tallafin fetur, ya shafi malamai da ma’aikatan Jami’o’in ƙasar nan.
Sannan kuma Sununu ya roƙi ɗalibai, iyaye da malamai su rungumi zaman lafiya, su guji aikata abin da zai rikita kalandar zangon karatu a Jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandare na faɗin ƙasar nan.
Ya ce Ma’aikatar Ilmi na tuntuɓar masu ruwa da tsaki wajen ganin an inganta rayuwar ɗalibai da malamai, ta hanyar samar da ababen more rayuwa a cikin jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandare.
Discussion about this post