Tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da na sanin wasu abubuwa da ya yi a lokacin yana shugaban kasa .
Adesina ya ce a lokacin da za su mika mulki, bayan gwamnati ta kare, ya zauna da shugaba Buhari na tsawon awa biyu muna tattaunawa.
” Buhari da bakin sa ya ce min akwai wasu abubuwa da ya aiwatar da bai yi su haka ba. Ya ce da ya san haka za su kasance da ba haka ya yi su ba.
Adesina ya ce kowani dan Adam na da abinda zai yi wa da-na-sani a rayuwa, dole.
Sai dai kuma Adesina ya kare shugaba Buhari bisa maganan canja launin Kudi da ya kirkiro da shi dab da zai sauka daga kujerar mulki.
” Wannan canj launin kudi da gwamnatin Buhari ta yi ya yi alfanu da yawa. Musamman ga masu karbar kudin fansa. Suma ‘yan bindigan sun shiga tsananin gaske na rashin kudi a hannu su. Wannan tsari da Buhari ya bijiro da ya yi matuklar tasiri.
Discussion about this post