Rundunar Ƴan sandan jihar Bauchi a ranar Juma’a ta bayyana cewa dakarun ta sun kashe mutum biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Jama’are
Rundunar ta kuma ce dakarun sun ceto mutum daya da har ya biya maharan da suka kama shi kudin fansana naira miliyan 10.
Kakakin rundunar Ahmed Wakili ya ce hakan ya faru a dalilin hadin guiwa da rundunar ta yi da jami’an tsaro dake jihar a daren Alhamis.
“Jami’an tsaron sun kama makamai da suka hada da manyan bindigogi kirar AK-47 uku, bindiga kirar SMG daya, adda daya da harsasai 105.
“Dakarun ‘yan sanda tare da hadin gwiwar mafarauta a Jama’are suka gano maboyar maharan.
“Jami’an tsaron sun kashe mutum biyar daga cikin maharan sauran kuma sun gudu.
Rundunar ta ce a ranar Laraban da ya gabata wasu mahara su 20 sun yi awon gaba da Wani Emeka Asogwa a gidan sa dake karamar hukumar Itas Gadau.
Kafin jami’an tsaro su ceto shi Asogwa ya biya madu garkuwan kudin fansa har naira miliyan 10.
Discussion about this post