Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya bayyana cewa matsawar Najeriya ta gaza kaiwa fagen cimma nagartacciyar dimokraɗiyya, to tamkar jinsin baƙar fata na duniya kakaf ne su ka gaza.
Da ya ke jawabi ga Taron Majalisar Ƙasa ta 10, Shettima ya yi kira gare su mutunta tsarin dimokraɗiyya, ta hanyar rungumar ra’ayoyi mabambanta domin ɗorewar nagartar dimokraɗiyya a Najeriya.
“Ita dimokraɗiyya ta na ƙara karsashi ne idan kowanen ku ya yarda kuma ya amince cewa ra’ayin kowanen ku ya na da muhimmanci da kuma tasiri,” inji Shettima.
Haka ya bayyana a Ikot Ekpene, Jihar Akwa Ibom, lokacin da ya ke buɗe Taron Sanin Makamar Aiki ga Shugabannin Majalisar Ƙasa.
Shettima ya jinjina buƙatar shugabanni su haɗa kai wajen rungumar jama’ar da su ke shugabanci a kan su. Kuma ya ce Allah ya albarkaci Najeriya da hamshaƙan mutane da manyan masu mulki.
“Mu tuna cewa shekarun da za mu yi nan gaba a kan mulki, ba za su kai yawan shekarun da za mu yi bayan mun sauka mulki ba. Saboda haka mu yi amfani da mulki domin mu amfana wa al’umma.
“Mu ne waɗanda su ka fi kowa samun sa’a a Najeriya. Amma ba wai don mun fi sauran maƙwautan mu ko makusantan mu ba.”
Haka Shettima ya shaida lokacin da ya ke buga misali da mafi hazaƙa a lokacin da ya ke Jami’ar Ibadan, amma a yanzu haka ya na can “ya na fama da gaganiyar rayuwa a wani bankin je-ka-na-yi-ka”.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya ce masu mulki wakilan al’ummar ƙasa ne kawai, amma ba don sun fi kowa cancanta ba.
Da ya ke nuna irin girma da ƙarfin Najeriya a duniya, ya yi magana a kan yawan al’ummar Najeriya, ƙasar da ta fi kowace ƙasa ta duniya. Sai ya ce, “Idan Najeriya ta gaza, to baƙar fata na duniya baki ɗaya ne su ka gaza.”
“Idan za a yi ƙididdiga, za a ga duk cikin mutum huɗu baƙaƙe a duniya, to 1 ɗan Najeriya ne. Don haka mu jajirce mu haɗa kai, mu ciyar da Najeriya gaba zuwa ƙasaitacciyar ƙasa.” Inji shi.
Discussion about this post