Shugaban Faransa Emmanual Macron, ya bayyana cewa Faransa ta kira jakadan ta da ke Nijar ya koma gida, kuma ta fara shirin kwashe sojojin ta da ke danƙare a Jamhuriyar Nijar.
Macron ya bayyana hakan a ranar Lahadi, ya na mai cewa, “Faransa ta yanke shawarar kwashe sojojin ta daga Nijar, kuma nan da sa’o’i kaɗan Jakadan Faransa da ke Nijar da sauran jami’an diflomasiyyar mu da ke Nijar, duk za su dawo gida.”
Haka Macron ya bayyana a wata hira da aka yi da shi, wadda aka yaɗa a talabijin.
Macron ya ce yarjejeniyar haɗin guiwar ayyukan sojoji da Faransa ta ƙulla da Nijar ta zo ƙarshe. Saboda haka dakarun Faransa da ke Nijar za su fara kwaso kayan su su dawo gida daga nan da ‘yan makonni kaɗan zuwa ‘yan watanni duk za a kammala kwaso su.”
Macron ya ce zuwa ƙarshen shekarar nan Faransa ba za ta bar ko soja ɗaya a cikin Nijar ba.
Aƙalla akwai sojojin Faransa 1,500 a cikin Nijar.
A baya gwamnatin sojojin Nijar ta umarci Jakadan Faransa da ke ƙasar ya fice daga Yamai, babban birnin ƙasar.
A lokacin Faransa ta ce Sojojin Mulkin Nijar ba su da damar korar jakadan da, tunda haramtacciyar gwamnati ce, wadda ta kifar da gwamnatin dimokraɗiyya, ta Mohammed Bazoum.
An yi ta ƙoƙarin ganin gwamnatin sojojin Nijar sun sauka sun maida Bazoum kan mulki, amma haƙar Faransa da ECOWAS ba ta cimma ruwa ba.
A na su ɓangaren, sojojin mulkin Nijar sun ce za su maida mulki ga farar hula nan da shekaru uku masu zuwa.
A na su ɓangaren, sojojin mulkin Nijar sun yi maraba da jin cewa Faransa ta maida jakadan ta gida, kuma za su fara shirin kwashe sojojin ta daga Nijar ɗin.
Discussion about this post