Shugaban jami’o’in Maryam Abacha, dake Kano da Maraɗi, jami”ar Canadian dake Abuja da Franco-British dake Kaduna Farfesa Adamu Gwarzo ya bayyana cewa jami’ar za ta fara dauka da karatu gadan-gadan nan da watanni uku masu zuwa.
Farfesa Gwarzo ya yi tattaki zuwa Kaduna inda ya kai ziyarar gani wa ido yadda ayyuka a jami’ar ke tafiya.
Da ya ke zazzagayawa , Farfesa Gwarzo ya yaba da irin ayyukan da ya gani ana aiwatar wa a jami’ar.
” Na zo Kaduna domin in ga yadda ayyuka ke gudana a jami’ar Franco-British. Ina so yadda muka ƙayata jami’ar Maryam Abacha dake Kano, haka muke so ta Kaduna ta zama.
” Za mu tabbatar da koma ya wanzu domin jin daɗin ɗalibai da malamai gabaki ɗaya.
Gwarzo ya kara da cewa da zarar an Kammala ayyuka nan da watanni uku, za a fara karatu gadan gadan a jami’ar.
Discussion about this post