Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta gabatar da wani magidanci wanda aka kama ya na yin shigar Kwamishinan ‘Yan Sanda a Legas.
Mutumin mai suna Emmanuel Nwagu, an kama shi ne a Hedikwatar ‘Yan Sandan Legas a lokacin da ya je domin ya yi ƙoƙarin ganin an saki wani mai laifi.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana wa manema labarai haka, ranar Litinin, lokacin da ya ke nuna wa ‘yan jaridar waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban, har su 13.
Yayin da wasu an kama su da yin sojan-gona, wasu laifin yi wa ƙananan yara fyaɗe, wasu satar mota, wasu safarar muggan ƙwayoyi, wasu kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Hundeyin ya ce an samu bindigogi huɗu, harsasai, agoguna, albarusai 11 da mota ɗaya a hannun waɗanda aka kama ɗin.
An kuma samu wayoyin hannu, tabar wiwi, muggan ƙwayoyi, wayar ‘oba-oba’ ta ‘yan sanda, katin shaidar aikin ɗan sanda, sai kuma hula da singileti na ‘yan sanda.
An damƙe kwamishinan ‘yan sandan na bogi a ranar 2 Ga Satumba a Hedikwatar ‘Yan Sanda.
A gidan sa kuma an je bincike aka samu katin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da wasu kayayyakin ‘yan sanda.
“Ɗan sandan bogin ya zo Hedikwatar ‘Yan Sanda kan sa tsaye, inda ya yi ƙoƙarin a saki wani ɗan fashi da muke tsare da shi.” Haka Hundeyin ya shaida wa manema labarai.
“Ya ce mana shi Kwamishinan ‘Yan Sanda ne. Da aka tambayi inda ya ke aiki da kuma wasu tambayoyin, to a nan aka gane kawai ɗan iska ne, aka damƙe shi.
“Bincike ta tabbatar da cewa ya daɗe ya na mu’amala da mutane a matsayin shi Kwamishinan ‘Yan Sanda ne. Kuma Allah kaɗai ya san iyakar farar hular da ya cuta a haka.”
Haka kuma Hundeyin ya shaida wa manema labarai kama wani lauya na bogi, mai suna Ibrahim Bello, wanda ya shafe tsawon shekaru da dama ya na damfarar mutane a matsayin shi lauya ne.
Ya kan yi shigar lauyoyi ya je kotu ya na buga-bugar tsayawa matsayin lauya da masu shari’a.
Shi ma a cikin harabar wata kotu aka damƙe shi.
An kuma gabatar wa manema labarai wata mai suna Ganiyat Oni, wadda ke sayar da muggan ƙwayoyi.
Hundeyin ya ce an samu kuɗi Naira 271,600 a hannun ta, waɗanda cinikin rana ɗaya ne, wato ranar da aka kama ta.
Discussion about this post