Kwamishinan Ilimi na jihar Kaduna ya bayyana cewa gwamnatin Kaduna karkashin Uba Sani za ta rage kudin makaranta shiga kwalejin Kapital School domin ‘ya’yan talakawa su samu shiga wannan makaranta.
Kwamishinan Ilimin jihar Farfesa Sani Bello, ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati ranar Alhamis. Farfesa Bello ya ce gwamnatin da ta shufe ta kara kudin makarantar daga naira 10,000 zuwa naira 65,000.
” Karin da gwamnatin El-Rufai ta yi daga naira 10,000 zuwa naira 65,000 ya sa yayan talakawa ba su iya shiba wannan makaranta. A dalilin haka tuni har mun aika wa gwamna takardar a rage kudin makarantar domin a bawa yara daman shiga wannan makaranta, ba sai lalai shafaffu da mai ba.
Bayan haka kuma ya ce gwamnati na shirin gina sabbin manyan makarantun zamani guda shida a Jere, Manchok, Rigachikum, Buruku da Pambegua.
Ya ce tuni har an ci karfin ginin wasu daga ciki.
A karshe ya ce gwamnati za ta gina wani bangare na kwalejin Ilimi dake gidan Waya a garin Hunkuyi domin rage tsadar tafiya da daliban yankin Arewacin Kaduna ke fama da shi zuwa can shiyyar Kudancin Kaduna don yin karatu.
Idan ba manta ba gwamnatin Kaduna a cikin wannan mako ta rage kudin manyan makarantu mallakar jihar. Da yawa daga cikin su an rage kusan kashi 50 cikin 100.
Gwamna Sani ya fadi haka da yake zantawa da gwamnati a farkon wannan wata.
Discussion about this post