Rundunar Ƴan sandan jihar Nasarawa ta kama wasu ma’aurata mata da mijin ta bisa laifin sace dan makwabcinsu mai shekara biyu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Ramhan Nansel ya sanar da haka wa manema labarai ranar Alhamis.
Nansel ya ce mahaifin yaron Adamu Abdullahi mazaunin Orange Market dake Maraba a karamar hukumar Karu Abuja a ranar 13 ga Agusta da misalin karfe 3:30 na rana ya kawo kara ofishin ƴan sanda cewa dansa mai shekara biyu ya bace makonni biyu da suka gabata.
“Abdullahi ya bayyana wa jami’an tsaron cewa a ranan wani ya kira shi a waya inda suke bukatar a biya su naira miliyan biyu kafin su saki yaron.
“Nan da nan jami’an tsaron suka fara gudanar da bincike inda suka kamo wadannan ma’aurata tare da wasu mutane uku.
“A hannun jami’an tsaro ma’auratan kuma makwabtan mahaifin yaron sun tabbatar cewa sune tare da hadin kan wasu mutane a Orange Market suka sace yaron.
“Mijin ya ce bayan sun saci yaron ne sai ya bai wa matarsa wanda ita kuma ta kai yaron jihar Katsina.
Nansel ya ce ‘yan sanda sun kama matan a jihar Katsina sannan sun ceto yaron kuma sun hada shi da Iyayen sa.
Bayan haka jami’in hulda da jama’a na rundunar ya ce ‘yan sanda sun kama batagari da ‘yan iska mutum 14 daga watan Yuli zuwa Agusta.
Ya ce rundunar ta kama wadannan mutane bisa ga laifuka da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane da ƴan kungiyar asiri.
Nansel ya ce sun kama da bindigogi da harsasai 11 a hannun su.
Discussion about this post