Shugaban majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya bayyana cewa majalisar ta karbi korafi game tsohon gwamnan Kaduna, Nasir E-Rufai, amma majalisar ba za ta tattauna a kai ba yanzu.
El-Rufai na daga cikin ministoci 28 da shugaban kasa Bola Tinubu ya aika wa majalisa domin a tantance su su zama ministocin sa.
Sanatoci sun tambayi El-Rufai yadda zai kawo matsalar wutar lantarki da ake fama da shi a kasar nan idan aka nada shi minista, El-Rufai ya ce ” gaba ɗaya harkar wutan lantarki a kasar nan na neman a yi masa garambawul ne.
” Tun daga, yadda aka sai da tasoshin samar da wutan lantarkin zuwa kamfanonin da ke rarraba wutan. Dole a koma ya a sake duba yadda suke gudanar da ayyukan su.
” Sannan kuma da matsalar iskar gas da ake fama da shi wanda ba ya isan tashoshin samar da wutar wanda dalilin haka ya sa ba su iya tura makamashin yadda ya kamata.
Daga karshe dai shugaban majalisan, Akpabio ya umarci tsohon gwamnan ya rusuna sannan ya kama gaban sa.
Discussion about this post