Sabon Ministan Harkokin Ilmi, Tahir Mamman, ya nemi haɗin kan ma’aikatan harkokin ilmi, tare da yin kira gare su cewa su shirya tashi tsaye a yi aiki ba ji, ba gani.
Mamman ya ce shi a rayuwar sa ya yi aiki wurjanjan tamkar wani birkilan da ke aikin gini. Saboda haka ya ce ƙalubalen bunƙasa harkokin ilmi su na da yawa da girman gaske.
Jim kaɗan bayan rantsar da su a ranar Litinin, Mamman tare da Ƙaramin Ministan Ilmi, Yusuf Sununu, sun kai ziyara a Ma’aikatar Harkokin Ilmi, inda ya gana da ma’aikata.
Sun samu tarba daga ma’aikata, shugabannin ɓangarori da na hukumomi da cibiyoyin ilmi, da kuma tawaga daga Jami’ar Baze da ke Abuja, inda Mamman ya ke aiki kafin a naɗa shi Minista.
Mamman ya nemi haɗin kan dukkan ma’aikata da shugabannin hukumomi da na cibiyoyin ilmi.
Sannan ya bayyana ma’aikatar harkokin ilmi a matsayin zuciyar bunƙasa ci gaba a Najeriya.
Ya jaddada masu cewa Gwamnatin Bola Tinubu na da mihimman ƙudirori da alƙawurran da ta ɗauka domin magance matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
“Alƙawurra da muradun su na da yawa waɗanda wannan gwamnatin ke so ta cimma. Shugaban ƙasar mu ya maida himma sosai wajen bunƙasa ƙasar nan.”
Daga nan sai ya roƙi ma’aikata cewa su taimake shi, shi da Karamin Ministan Ilmi Sununu domin su ciyar da ɓangaren ilmi gaba sosai.
Ya ƙara da cewa kyautata walwala da jin daɗin ma’aikata ne zai kasance abin bai wa muhimmanci sosai a ƙarƙashin sa.
“Ni aiki na ke yi wurjanjan kamar birkila. Shin yaya birkila ke aikin gini? A duk lokacin da ya je wurin aikin gini, leburori za su riƙa miƙa masa kamar bulo 100 ko 200 a ranar. Ya na so ya ga gini ya ɗaga sama sosai.
“Saboda haka a cikin watanni uku zuwa shida, sai ka ga har an gida gida. Saboda haka mu ma za mu yi aiki wurjanjan mu gina harkokin ilmi a faɗin Najeriya.”
Sabon ministan ya ce ya shafe tsakanin shekaru 35 zuwa 40 ya na aiki a ƙarƙashin gwamnati da kuma wurare masu zaman kan su.
Mamman ya aminta da cewa akwai babban ƙalubale a gaban sa, “amma ina tabbatar maku cewa za mu bi duk wasu haƙƙoƙin da suka dace ku ci moriyar su.”
Discussion about this post