Ƙungiyar Ƙwararrun Injiniyoyi Mata ta Najeriya (APWEN), ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba su damar aikin gyara matatun fetur ɗin ƙasar nan.
Sun yi wannan kira ne a ranar Asabar, a wurin wata lacca da suka gabatar, lokacin taron ƙungiyar na shekara-shekara, a Ikeja, Legas.
Shugabar Ƙungiyar ta Jihar Legas, Atinuke Owolabi ce ta bayyana haka, jim kaɗan bayan zaɓen ta da aka yi a wurin taron.
Atinuke ta ce tabbas, injiniyoyi mata daga ɓangaren ƙwararru daban-daban za su iya gyara matatun fetur ɗin a cikin shekara ɗaya kacal.
“Dukkan ƙwararrun injiniyoyi mata a shirye su ke su haɗa kai domin ganin cewa sun gyara matatun fetur ɗin Najeriya, waɗanda tsawon shekaru da dama ba su aiki.
“Saboda haka mu na yin kira ga Shugaban Ƙasa ya bai wa Injiniyoyi mata wannan ƙalubalen, domin su farfaɗo da matattun matatun ɗanyen man fetur ɗin ƙasar nan. To kuma ina tabbatar maku za mu iya gyara su a cikin shekara ɗaya, da yardar Allah,” inji ta.
Ta ce duk ƙasar da ke son ci gaba, to fa tilas sai ta tallafa wa injiniyoyin ta na cikin gida.”
Gwamnatin Buhari dai ta yi alƙawarin gyara matatun ƙasar nan da ke Warri, Fatakwal, Legas da Kaduna.
Sai dai kuma bayan da gwamnatin ta shafe shekaru takwas kan mulki, hakan bai yiwu ba, sai ma biliyoyin nairorin da aka riƙa ɗibga asara ana kashewa a matatun kowace shekara.
Discussion about this post