Kotu dake Igboro a Ilorin jihar Kwara ta raba aure da ke tsakanin Hafsat Bashir da Bashir Abdullahi saboda rashin kula.
Hafsat ta shigar da karar mijinta saboda rashin kula da ita da ba ya yi da kuma kin biya mata bukatu.
Alkalin kotun AbdulQadir Umar ya raba auren a dalilin dagewa da Hafsat ta yi na lallai ta gaji da zaman aure tsakaninta da Bashir duk da kuwa akwai ‘ya’ya hudu a tsakanin su.
Bashir ya fadi a kotun cewa baya so ya rabu da matarsa amma tun da ta matsa kan su rabu zai iya bada ‘ya’yan sa kanana biyu cewa shi zai rike manya biyu a domin karatun su.
Umar ya bai wa Hafsat ikon kula da ‘ya’yan su uku sannan ya umarci Bashir cewa zai biya kudin ciyar da ‘ya’yan sa da kudin makarantan su duka.
Discussion about this post