Rundunar ‘yan sandan a jihar Legas ta kama wani fasto mai shekaru 43 bisa laifin damfarar abokin sa naira miliyan 105.
Mataimakin Sifeto-Janar din ‘yan sanda da ke kula da shiyar zone 2 Ali Mohammed ya ce faston ya yi wa mata da ‘ya’yan abokinsa asiri ya canja sunayen su zuwa na sa domin ya mallaki dukiyoyin su.
Mohammed ya ce faston ya aikata hakan ne tare da taimakon matarsa.
Ya ce rundunar ta samu labarin abinda ya faru bayan karar da da wanda aka damfara dake zama a kasar Amurka ya kawo ofishin ‘Yan sanda.
“ Ya shaida wa jami’an tsaro cewa faston ya dauki shekaru kusan 10 yana damfaran sa kudi. Ya damfare sa akalla naira miliyan 105.
Mohammed ya ce bayan ya shiga hannu faston ya fadi wa jami’an tsaro cewa ya aikata haka ne bisa umarnin Ruhu Mai Tsarki.
Ya ce matar faston ita ma ta tabbatar wa jami’an tsaro cewa ta karbi kudi har naira miliyan 11.8 daga hannun abokin mijinta.
Mohammed ya ce zuwa yanzu faston da matarsa da wasu mutum biyar da suka taya su damfarar mutumin na tsare a ofishinsu.
Ya ce rundunar ta kwato motoci Toyota Venza 2009, Bas da filaye da gidaje na abokin daga hannun faston.
Mohammed ya ce rundunar za ta ci gaba da bincike akai.
Discussion about this post