Yayin da talakawa musamman a Arewacin Najeriya ke fama da raɗaɗin tsadar rayuwa, tun bayan cire tallafin fetur, wata sabuwar guguwar matsayin rayuwa kuma ta dabaibaye dubun-bubatar manoman da suka ci Bashin Anchor Borrowers, wanda Gwamnatin Tarayya ta bai wa manoma tun shekaru takwas da suka gabata.
Bankin CBN ya raba bashin noma na sama da naira tiriliyan 1, amma har yanzu an kasa karɓo sama da naira Biliyan 503 daga hannun waɗanda aka bai wa lamunin.
A cikin watan Yuli, ranar wata Litinin, Kotun Majistare ta Birnin Kebbi ta ɗaure wani mai suna Usman Muhammad, saboda ya karɓi lamunin, amma ya kasa biya.
Usman na ɗaya daga cikin mutane sama da 70,000 suka amfana da lamunin a Jihar Kebbi kaɗai. Usman ya karɓi lamunin shekaru shida da suka gabata.
Yarjejeniyar ƙa’idar biyan bashin dai ita ce manomi zai biya da amfanin gona na adadin kuɗin da ya karɓa da kuma ɗan kuɗin ruwan da aka ɗora masa.
Usman ya ce, “Ban ci ribar ko sisi ba. Duk amfanin gonar da na shuka ambaliya ta yi gaba da shi.”
Haka Muhammad ya shaida wa PREMIUM TIMES, wanda a ranar da aka yanke masa hukuncin ɗauri, sai wani kawun sa ya biya wasu kuɗaɗen, aka yi yarjejeniya da shi a kotu cewa zai biya sauran can gaba.
Dubban manoma na su biya bashin ba, wanda an ƙirƙiro shirin ne domin bunƙasa noma da samar da abinci a wadata. Sai dai kuma maimakon a samu nasara, an wayi gari daga lokacin da aka ƙirƙirar shirin zuwa yanzu, farashin kayan abinci kamar shinkafa ya nunka sau biyu.
Zuwa 2022, aƙalla manoma miliyan 4.8 ne suka amfana da shirin Bayar da Lamunin Noma na ‘Anchor Borrowers’, na CBN.
Da yawan waɗanda suka kasa biya sun ɗora dalilin su kan ambaliya, matsalar tsaro, canjin yanayi da sauran su.
Sai dai wasu masana sun ce da yawa sun ƙi biya ne, saboda su ka ganin cewa lamunin da suka karɓa, wani rabon su ne ya faɗo masu har gida daga arzikin Najeriya.
Akwai kuma rahotonnin da suka tabbatar da cewa wasu da dama aure su ka yi, ko suka ƙara da kuɗaɗen bashin da su ka karɓa. Wasu kuma an ce sun riƙa amfani da kuɗaɗen su na zuwa aikin Hajji a Saudiyya.
Tsohon Shugaban Ƙungiyar Masu Noman Shinkafa ta Jihar Kebbi, Sahabi Augie, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “mun yi bakin ƙoƙarin karɓo basussukan, amma abin ya faskara. Dalili kenan muka bi matakin hukuma a kotu.
“Shi ya sa yanzu a Jihar Kebbi duk wata Kotun Majistare mun bi mun bayar da sunayen waɗanda su ka karbi basussukan, amma ba su biya ba.
‘Shirin Lamunin CBN Ga Manoma shiririta ce, kashi 24% kacal su ka biya bashin’ – IMF:
Hukumar Bada Lamuni ta Duniya, IMF, ta bayyana cewa Shirin Lamunin CBN ga Manoma, wato ‘Anchor Borrowers Program’, ABP, ko kaɗan bai bunƙasa fannin noma ba, saboda ba a bayar da lamunin ga ainihin manoma na gaskiya waɗanda ya kamata a bai wa lamunin ba.
IMF ya ce saboda waɗansu ne can daban aka bai wa lamunin, ba manoma gangariya ba, shi ya sa har yanzu sun ƙi biyan basukan, sai kashi 25% bisa 100% na waɗanda waɗanda suka karɓi lamunin su ka biya.
Cikin watan Nuwamba, 2015 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙirƙiro Shirin Bayar da Lamuni Ga Ƙananan Manoma, a ƙarƙashin Babban Bankin Najeriya (CBN), da nufin bunƙasa harkokin noma a hannun ƙananan manoma.
A ƙarƙashin tsarin dai CBN ta riƙa bayar da lamunin noma bisa sharaɗin cewa Duk kayan gonar da su ka noma, za su kwasa su kai wa jami’an ABP su saya, a yi ciniki su ɗebe wa gwamnati kuɗaɗen da ta ramta masu.
An umarci ƙananan manoma su riƙa noma shinkafa, masara, alkama, auduga, rogo, doya, rake, ‘ya’yan itace, tumatir da kuma kiwon dabbobi, tsuntsaye da kifi.
An riƙa bada lamunin a ƙarƙashin wasu ƙananan bankunan tallafa wa masu ƙananan masana’antu, wato ‘Microfinance Banks’, wato MDBs.
Sai dai kuma IMF tmya bayyana cewa a binciken sa, waɗanda ya kamata a riƙa bai wa lamunin kuɗaɗen ba su aka riƙa bai wa ba.
Bankin ya ce shi ya sa shirin duk da ya hana shigo da wasu kayan abinci daga waje, bai kawo sauƙi ga abincin da ake nomawa a cikin gida ba, sai ma tsawwalawa da farashin kayan abinci ke ci gaba da yi, a duk wata ko ƙasa da haka.
Ya ce kashi 24 bisa 100 kaɗai su ka biya lamunin.
Wani rahoto da PREMIUM TIMES Hausa ta taɓa bugawa a baya, an gano yadda wasu da dama su ka riƙa ƙara aure da kuɗaɗen lamunin, wasu kuma sun riƙa kwasar kuɗaɗen su na zuwa aikin Hajji ko Umra.
Discussion about this post