Akalla mutane 4 ne suka rasu a hadarin ruftawar ginin masallacin fadar masarautar Zazzau.
Maimartaba Sarkin Zazzau Ahmed Bamali, ya tabbatar da aukuwqr lamarin yayin da ya ce za a yi jana’izar wadanda suka easu a fadar da karfe 8 na daren Juma’a.
Sarkin ya yi karin bayani cewa dama ana gab da gyara masallacin ne wannan abu ya auku, daga nan sai ya umarci masu sallah su yi sallah a wajen masallaci zuwa har a gyara.
Wasu da suka zanta da wannan karida sun ce ginin ya rufta a kan masallata ne a lokacin sallar la’asar.
A bidiyo da aka yada a shafukan yanar gizo an ga masallata da wasu matasa sunnkawo dauki domin ciro mutanen da gini ya rifta a kan su.
Masallacin Juma’ar fadar masarautar Zazzau masallaci ne da sarakunan Zazzau suke sallah a ciki. Daɗaɗɗen masallaci ne da ke neman gyara.
Byan mutum huɗu da suka rasu, akwai wasu mutum 7 da suka samu rauni.
Discussion about this post